Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Tuchel ya ja ragamar wasa 13 ba a doke shi ba a Chelsea

 117614486 Thomastuchelgettyimage Kocin Chelsea Thomas Tuchel

Thu, 18 Mar 2021 Source: BBC

Chelsea ta kai wasan quarter finals a gasar Champions League ta bana, bayan da ta doke Atletico Madrid 3-0 gida da waje.

A wasan farko da suka fafata cikin watan Fabrairu, Chelsea ce ta yi nasara da ci 1-0, kuma Olivier Giroud ne ya ci kwallon.

Kawo yanzu kocin Chelsea, Thomas Tuchel ya ja ragamar wasa 13 a dukkan fafatawa ba tare da an doke shi ba ya ci wasa tara da canjaras hudu.

Tuchel din shi ne na farko a wadan da suka ja ragamar Chelsea da ya yi karawa da yawa ba tare da yin rashin nasara ba.

Kocin dan kasar Jamus ya koma Stamford Bridge cikin watan Janairu daga Paris St Germain, inda ya maye gurbin Frank Lampard, wanda a lokacin Chelsea ke mataki na tara a teburin Premier.

Bayan Chelsea da take cikin kungiyoyi takwas da za a raba jadawalin Quarter finals da wasan daf da karshe ranar Juma'a, har da Liverpool da kuma Manchester City daga Ingila.

Sauran wadanda suka kai zagaye na uku a gasar ta zakarun Turai ta bana sun hada da Real Madrid da Paris St Germain da Porto da Borussia Dortmund da mai rike da kofin Bayern Munich.

Source: BBC