Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Limaman da za su jagoranci sallar Taraweeh da Tahajjud a masallancin Harami a bana

 117700566 Untitleddesign.png Labarai wai limamai shida ne za su jagoranci gudanar da sallolin a bana

Thu, 25 Mar 2021 Source: BBC

Hukumomin Saudiyya sun fitar da jerin sunayen limaman da za su jagoranci sallolin Tarawi da Tuhajjud a masallacin Harami da ke birnin Makka a lokacin azumin bana.

Shafin intanet na Haramain Sharifain ya bayyana cewa limamai shida ne za su jagoranci gudanar da sallolin a bana.

Ana sa ran za a fara Azumin wannan shekarar a cikin watan Afirilu mai zuwa.

Har wa yau, hukumomin Saudiyya sun ce bana babu wasulLimamai da za a gayyato domin limancin sallolin, kamar yadda ake gani a shekarun da suka gabata.

Babban limamin masallacin Ka'abah Sheikh Abdul Rahman al-Sudais na daga cikin limaman da hukumomin suka ce za su yi jagorancin sallolin.

Ga hotunan limaman da za su ja ragamar sallolin Tarawi da Tuhajjud.

Source: BBC