Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Ƙasa ta rufta da masu haƙar ma’adinai a Guinea

 99843514 Mining Akalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu sakamakon zaftarewar kasa a Guinea

Tue, 11 May 2021 Source: BBC

Akalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu sakamakon zaftarewar kasa da ta afku a wani wurin hakar zinare a yankin Siguiri da ke arewa maso gabashin Guinea.

Duwatsu sun faɗo a safiyar ranar Asabar, suka murƙushe wasu tare da binne wasu a cikin mahakan.

Mai magana da yawun gwamnati ya ce "za a gudanar da bincike kan ainihin musabbabin al'amarin da kuma abin da ya haifar da shi".

Wani jami'in kungiyar agaji ta Red Cross ya ce akwai mata biyu daga cikin waɗanda suka mutu kuma akwai yiwuwar za a samu karin gawarwakin.

"An haki wurin nan da injina ya zaizaye. Masu hakar sun yi nisa a cikin ramukan da suke haka. Abin da ya janyo wannan mummunar zaftarewar kenan," kamar yadda Djanko Dansoko ya bayyana a shafin Guinee360.

Akwai daruruwan masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a yankin Siguiri, inda akan iya hako zinare da hannu sai dai wajen cike yake da hadari.

Wurin da wannan abu ya faru yana kusa da kauyen Tatakourou ne, mai nisan kilomita 40 daga tsakiyar Siguiri.

Shekara biyu baya masu hakar ma'adanai 17 ne suka mutu a Guinea, haka zalika wasu gwammai sun kara mutuwa watanni tara baya.

Masu hakar zinare ba bisa ka'ida ba sun mamaye wannan wuri daga kasashen Mali da Senegal da wasu kasashen yammacin Afrika.

Source: BBC