Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Amurka da Japan sun yi Allah-wadai da Koriya Ta Arewa kan sabon gwajin makami mai linzami

 117715466 Hi066431264 Amurka da Japan da Koriya Ta Kudu duk sun yi Allah-wadai da gwajin

Ven., 26 Mars 2021 Source: BBC

Koriya Ta Arewa ta yi ikirarin cewa makamai masu linzamin da ta ƙaddamar ranar Alhamis wasu nau'in "sabbin makaman ne da ake harbawa daga jikin bindiga da nufin ƙara karfin sojinta."

Koriyan ta fadi hakan ne a wata sanarwa ta farko da ta fitar tun bayan yin gwajin.

Wannan ne karo na farko da ƙasar ta harba makaman a cikin kusan shekara ɗaya, kuma na farko tun bayan da Joe Biden ya zama shugaban ƙasar Amurka.

Mista Biden ya ce Amurka za ta "mayar da martani yadda ya dace". Amurka da Japan da Koriya Ta Kudu duk sun yi Allah-wadai da gwajin.

A ƙarƙashin ƙudurorin da aka cimma na Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, an haramta wa Koriya Ta Arewa gwajin makamai masu linzami.

Sanarwar da ƙasar ta fitar a ranar Juma'a da ta fito daga kafar yaɗa labaran ƙasar KCNA, ta ce makaman biyu na gwajin an harba su ne da nufin yin tafiyar kilomita 600 daga gabashin gaɓar tekun Koriya Ta Arewan, inda bayanin ya ci karo da ƙiyasin Japan na cewa sun haura fiye da kilomita 400.

Ya ƙara da cewa sabon makamin yana iya ɗaukar abu mai nauyin tan 2.5, wanda zai iya ba shi damar ɗaukar kayayyakin makaman ƙare dangi.

An ambato Ri Pyong Chol, wani babban jami'i a ƙasar wanda aka yi gwajin a gabansa yana cewa: "Samar da wannan tsarin makamin abu ne mai matuƙar muhimmanci ga bunƙasar ƙarfin sojinmu da daƙile duk wata barazana ta soji."

Sai dai shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un ba ya wajen lokacin da aka harba makamin.

Tambayar da nake yawan yi ita ce me ya sa Koriya Ta Arewa ke yin gwajin a yanzu?

Babu amsa mai sauƙi ta wannan tambaya. Na farko saboda za su iya, kuma Koriya Ta Arewa na da sabbin makaman da za ta gwada.

Amma saƙonnin baya-bayan nan da Koriya Ta Arewa ke gargaɗin Amurka da ka da ta "tunzura ta" kuma gwamnatin Biden za ta "ɗanɗana kuɗarta" to akwai abin da Arewar ke nufi da hakan.

Hukumar leƙen asiri ta Koriya Ta Kudu ta ce ta yi amanna Koriya Ta Arewa ta harba makaman ne a daidai lokacin da Shugaba Biden ke daf da gaatar da taron manema labarai.

Ta kuma yi amannar cewa Arewar ta yi hakan ne don nuna adawa da miƙa ɗan ƙasarta Mun Chol Myong ga Amurka daga Malaysia, da kuma matakin Hukumar Kare Haƙƙin Dan adam ta MDD na baya-bayan nan mai adawa da Koriya Ta Arewa.

Ko ma dai mene ne dalilin, saƙon da Koriya Ta Arewa ke aike wa duniya ya sha bambam da wanda take aike wa al'ummarta.

Shafin farko na jaridar ƙasar ya nuna Kim Jong-un yana duba sabbin motocin bas-bas na fasinja - ba a ganshi a wajen gwajin makaman ba.

Mista Kim ya na motsa ƙwanjinsa ne a idon duniya amma a idon mutanensa yana nuna shi mai kawo musu sauyi ne.

Mr Biden ya shaida wa manema labarai cewa harba makaman keta yarjejeniyar MDD ne, kuma Amurka na tuntuɓar abokan hulɗa da ƙawayenta.

"Za a mayar da martani - idan har suka sake ta'azzara lamarin, za mu mayar da martani yadda ya dace," in ji shi.

"Amma kuma a shirye nake ga yin wani abu da ya shafi diflomasiyy, amma dole ya kasance akwai sharaɗi kan lalata makaman nukiliya.

Source: BBC