Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Ronaldo, Pogba, Jesus, Kane, Ceballos da Pochettino

 118728384 Ronaldoindexresize Cristiano Ronaldo, dan kwallon Juventus

Sun, 30 May 2021 Source: BBC

Manchester United na sa ido kan Cristiano Ronaldo, dan wasan Juventus da Portugal mai shekara 36, domin tana son musanya shi da Paul Pogba, dan wasan tsakiya mai shekara 28. (Gazzetta dello Sport via Express)

Tottenham ana sha'awar dauko Gabriel Jesus dan wasan kasar Brazil mai shekara 24 daga Manchester City, kuma wannan zai bayar da damar sauya shi da Harry kane ami shekara 27 . (Star)

Dani Ceballosdan wasan Real Madrid mai shekara 24 na son ci gaba da zamansa a kungiyar a kakar wasa mai zuwa, ko kuma ya bar ta gaba daya, bayan ya shafe shekara biyu a matsayin dan aro a Arsenal. (Mail)

Kungiyar Burnley na son dauko Joe Worrall, dan wasan Nottingham Forest mai shekara 24 kan fam miliyan 10. (Sun)

Ajax na sha'awar zawarcin dan kwallon Tottenham da tawagar Netherlands, Steven Bergwijn. (De Telegraaf - in Dutch)

Dan wasanReal Madrid, Raphael Varane, wanda ake alakanta shi da cewar zai koma Manchester United, ya ce a yanzu hankalinsa na tawagar Faransa da kofin nahiyar Turai, babu batun zama ko barin kungiya a yanzu haka a gabansa. (Mail)

West Ham United ta sanar da Fabian Balbuena cewar zai iya neman wata kungiyar domin gwada sa'a da zarar kwantiraginsa ya kare a karshen watan Yuni. (Football Insider)

Aston Villa na son daukar dan kwallon Burnley, Dwight McNeil da na Norwich City, Emiliano Buendia. (The Athletic - subscription required)

Tsohon dan wasan Chelsea, Oscar nason sake komawa Stamford Bridge da taka leda - bayan shekara hudu da ya koma kungiyar China Shanghai Port. (Goal)

Brighton tana tattaunawa da dan wasan Ajax, Kjell Scherpen kan kudi fam miliyan hudu. (The Athletic)

Ana hasashen cewar tsohon kocin Wolverhampton Wanderers, Nuno Espirito Santo shi ne zai karbi aikin horar da Lazio bayan daSimone Inzaghi ya bar kungiyar Serie A da ake cewar zai koma Inter Milan da horar da tamaula. (Calciomercato - in Italian)

Source: BBC