Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Yadda za a inganta tsarin haihuwa tsakanin ma'aurata

 118502809 Gettyimages 1232843439 Masana na ci gaba da bincike inganta tsarin haihuwa

Sun, 30 May 2021 Source: BBC

A cikin makonni biyu da suka gabata manyan kasashe biyu na duniya sun gamu da wata matsala - sakamakon ƙidayar jama'a a Amurka da China ya nuna cewa akwai yiwuwar kasashen biyu za su fara fuskantar raguwar jama'a raguwa na kusa fiye da yadda suke tsammani.

Hakan ya faru ne saboda raguwar da aka samu a yawan haihuwa. Yayin da hakan ke faruwa, yawan tsoffi ya ƙaru abin da ke kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki.

Wani abu ne da galibin gwamnatoci ke son kaucewa.

China da Amurka ba su kai wannan lokacin ba tukun. Amma za su iya koya daga wasu kasashe da tuni suke tunanin yadda za su inganta tsarin haihuwa.

Wata babbar matsala ce da ba ta da maslaha cikin sauki. Wasu kasashe irin Rasha sun yi kokarin bai wa iyaye kyautar kudi domin jan ra'ayinsu su haihu.

Amma tsare-tsare irin haka da wuya su yi tasiri - iyaye na bukatar wani tsarin na daban. Toh ta ya ya gwamnati za ta ja ra'ayin mutane don su haihuwa?

1. A bai wa iyaye cikakkiyar kulawa cikin sauƙi

Cikin shekara tara garin Nagi-cho ya samu nasarar ninka yawan haihuwar da ake yi daga yara 1.4 zuwa 2.8 da kowace mace za ta haifa hadi da tsarin kula da lafiya da ya yi dai-dai da iyali.

Iyalai na samun tagomashi da alawus-alawus na yaransu amma iyaye na biyan kusan rabin kudin wajen tura yaro makaranta. A sauran yankin Gabashin Asiya, durkushewar al'adun aiki ya sa abu ne mawuyaci iyaye mata ko maza su iya daidaita bukatun aiki da na iyali.

Koriya Ta Kudu na daya daga cikin kasashen da ke da karancin haihuwa a duniya sannan tana kashe sama da dala biliyan 130 wajen kyautatawa iyalai - ba da kulawa kyauta ga yara da tallafawa mata masu yoyon fitsari.

Kim Ji-ye mace ce da aikinta shi ne tallacce-tallace a Seoul. Ba ta da sha'awar haihuwa amma sai da ta biyewa matsin lamba daga iyayenta - yanzu yayanta maza uku.

Duk da cewa tana samun tallafin kula da jarirai daga gwamnati, ba ta yadda irin wadan nan kudaden sun yi wani tasiri a matakinta.

Akwai karancin wuraren kula da yara na gwamnati a manyan birane - sannan wuraren kula da yara masu zaman kansu na da tsada.

"Ban taba son na kara haihuwa ba," in ji ta. "Rainon yaro ko daya ne, Yana da matukar wahala don haka ina son na mayar da hankalina a kansa."

"Babu daya daga cikin tsare-tsaren gwamnatin nan da ya kawo sauyi kan tsarin aiki a sassan gabashin Asia da ke cin karo da tsarin iyali.

"A Koriya, muna da tsarin aiki a shari'ance da kuma hutun da ake bai wa mai jego da uba," in ji Erin Hye Won Kim, wani Farfesa a Jami'ar Seoul wanda yake nazari kan haihuwa a yankin.

2. A saukaka yanayin aiki

South Korea da China da Japan na wuce gona da iri amma a akasarin kasashen da suka ci gaba tsarin aiki ya ci karo da rayuwar iyali.

Wani zabi da aka bai wa gwamnati shi ne ta yi kokarin ba da damar yin aikin wucen-gadi. Kasashen da suke kan wannan tsarin suna samun yawan haihuwa.

Amma mafi yawan lokaci mata ne ke yin irin wannan aikin na wucen gadi.

Abu ne mai yiwuwa a samu mata na aiki kuma a samu haihuwa. Sweden kasa ce da ake jinjina mata saboda tsare-tsarenta da suka yi dai-dai da iyali ba wai kawai a gwamnati ba har ma a kasuwanci.

"Muna da fahimta cewa a wani lokaci na rayuwarsu, maza da mata na da yaran da ba su da yawa sannan wani lokacin dole ne su koma gida da wuri," in ji Farfesa Gunnar Andersson, malami a Jami'ar Stockholm.

Kuma akwai wasu hanyoyi na saukaka aiki ba tare da rage yawan sa'oin da ake shafewa ana aiki ba.

Wani bincike da aka yi a 2017 ya nuna cewa samun intanet mai karfi a Jamus ya yi dai-dai da yawan haihuwa tsakanin mata masu ililmi.

Mata masu yin aiki daga gida sun gano za su iya zama tare da yayansu da kuma zabin kara haihuwa. Ba a iya samun irin wannan tasirin a tsakanin matan da suke da karancin matakin ilimi da kuma maza.

A cewar Farfesa Anna Rotkirch wadda yake bai wa gwamnatin Finland shawara kan haihuwa, akwai makamancin irin wannan tsari da ke tafiya sosai a kasar.

Kasar ta fuskanci raguwar yawan haihuwa a shekarar da ta gabata ta hanyar kara yawan haihuwa a lokacin annoba.

Farfesa Rotkirch na ganin tsarin ilimin Finland yana da rawar takawa saboda komawa tsarin karatu ta intanet na tafiya lafiya lau.

Amma ta gano wani abu daban - akwai banbanci sosai kan yadda mata a sassan Turai suke tattauna batun aikin daga gida da hadawa da kula da yara.

"Abin da na samu daga Burtaniya shi ne mata sun kagu da batun karatu daga gida sannan mazajensu ba sa tallafawa sannan ga suka suka game da batun daidaiton jinsi." Duk da cewa tana da yara, ba wai batu bane da ta taba ji a Finland.

3. A sa maza su yi aiki daga gida

A kowace kasa da aka gudanar da bincike, bayanai sun bayyana cewa mata sun fi lokacin hutu a kan maza saboda sun fi yin aikin da ba a biyansu a gida.

Erin Hye Won Kim a jami'ar Seoul ya gano cewa an samu karuwar haihuwa lokacin da maza suka taimaka musu da aikin gida.

Ta yi nazari kan iyalai masu yara daya sannan ta gano cewa idan maza suka yi karin sa'a daya suna aiki a gida, hakan zai kara yiwuwar samun karuwar yaro na biyu.

A Sweden, an samu karuwar haihuwa a shekarun 2000 saboda saukaka kula da lafiyar yara.

Amma iyaye maza da mata ma ana basu hutu idan suka samu karuwar jariri. Iyaye maza na daukan kashi 30 na ranakun aikinsu suna hutu kamar yadda matan da suka haihu suke yi.

"Suna daukar nauyin kula da yaro cikin shekara daya da rabi da haihuwarsa."

A Sweden, kashi 73 cikin 100 na mata na yin aikin gida ko girki na kusan sa'a daya kowace rana sannan kashi 56 cikin 100 na maza sannan a Turai, kashi 74 cikin 100 ne na mata sannan maza na da kashi 34 cikin 100.

"Ina ganin sakonnin da kuke turawa suna da mahimmanci," in ji Farfesa Rotkirch.

Cikin shekara 10 da ta gabata, yawan haihuwa a Scandinavia ya ragu. A Sweden, ana samun raguwar yawan haihuwa amma a Norway da Finland ya fadi warwas.

Shin yana da mahimmanci?

Yawan haihuwa a Yammacin Turai ya yi kasa tun shekarun 1970 amma ana samun karuwar yawan al'umma. "Yawan jama'a na karuwa sanadin kaura," in ji shi.

Raguwa a yawan al'umma na da tasiri ga batun sauyin yanayi. "A yanzu haka ba ma haihuwa kamar lokacin iyayenmu da kakanni." in ji Farfesa Leeson

Akwai kuma fa'idojin da gwamnatoci ke samu game da batutuwan haihuwa. Lokacin da Koriya ta Kudu ta bijiro da dokar lokacin aiki, rage makwannin aiki daga sa'a 44 zuwa 40.

Erin Hye Won Kim ta gano cewa maza sun fi daukan lokaci wajen kai ziyara da tallafawa tsoffin iyayensu.

Ya kamata a samar da tsare-tsare na taimaka wa mutane su samu yawan yaran da suke so, in ji Farfesa Rotkirch.

"Suna tasiri a lafiyar yara da lafiyar mutanen da suke da yara. Kuma watakila wannan ne mafi mahimmanci cewa yaran da aka haifa sun samu rayuwa mai kyau."

Source: BBC