Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Rohr ya fayyace rawar da Ahmed Musa zai taka a Super Eagles

 117520160 Rohrandmusa Rohr ya ce an bai wa kyaftin Ahmed Musa gurbin girmamawa

Thu, 11 Mar 2021 Source: BBC

Gernot Rohr ya ce an bai wa kyaftin Ahmed Musa gurbin girmamawa na musamman a tawagar Najeriya da za ta kara da Benin da Lesotho.

Super Eagles za ta buga wasannin neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da kasashen biyu cikin watan Maris, don zuwa gasar da Kamaru za ta karbi bakunci.

Bayan da aka bayyana sunan Ahmed Musa, cikin tawagar Najeriya, hakan ya sa ake cece kuce kan dan kwallon da ba shi da yarjejeniya da wata kungiya tun Oktoba da ya bar Al Nassr ta Saudi Arabia.

Hakan ne ya sa Rohr ya fayyace rawar da Musa mai shekara 28 zai taka a Super Eagles a wasa biyu da za ta kara.

"Musa zai taka rawar gani a cikin 'yan wasan da muka gayyata a fafatawar da za muyi da Benin da kuma Lesotho a wasannin neman zuwa kofin nahiyar Afirka.

"Mun gayyace shi a matakin kyaftin kuma shi ne na 24, amma ba zai buga wasannin da zamu yi ba."

Sai dai ba a gayyaci Odion Ighalo ba wanda ke taka leda a Saudi Arabia, wanda Rohr ke kiransa da ya dawo bugawa Nijeriya tamaula, bayan ritaya da ya yi.

Nigeria za ta ziyarci Benin ranar 22 ga watan Maris a wasan daga karshe ta karbi bakuncin Lesotho ranar 30 ga watan Maris, shi ne wasa na karshe a cikin rukuni.

Najeriya wadda ta lashe kofin nahiyar Afirka karo uku ita ce ta daya a rukuni na 12 da naki takwas, sai Benin mai maki bakwai, Saliyo da maki uku da kuma Lesotho mai maki biyu.

Tawagar Super Eagles da aka gayyata:

Masu tsaron raga: Francis Uzoho (APOEL Nicosia, Cyprus) da John Noble (Enyimba FC) da kuma Maduka Okoye (Sparta Rotterdam, The Netherlands)

Masu tsaron baya: Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain) da Leon Balogun (Glasgow Rangers, Scotland) da Chidozie Awaziem (Boavista, Portugal) da William Troost-Ekong (Watford, England) da Olaoluwa Aina (Fulham FC, England) da Jamilu Collins (SC Padeborn, Germany) da Zaidu Sanusi (Porto, Portugal) da kuma Tyronne Ebuehi (Twente, The Netherlands).

Masu buga tsakiya: Oghenekaro Etebo (Galatasaray, Turkey) da Wilfred Ndidi (Leicester City, England) da Abdullahi Shehu (Omonia Nicosa, Cyprus) da Joseph Ayodele-Aribo (Glasgow Rangers, Scotland) da kuma Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, England).

Masu cin kwallaye: Alex Iwobi (Everton, England) da Sadiq Umar (Almeria, Spain) da Samuel Chukwueze (Villarreal, Spain) da Victor Osimhen (Napoli, Italy) da Kelechi Iheanacho (Leicester City, England) da Samuel Kalu (Girondins Bordeaux, France) da kuma Moses Simon (Nantes, France).

Gurbi na musamman: Ahmed Musa

Masu jiran ko ta kwana: Daniel Akpeyi (Kaizer Chiefs, South Africa) da Henry Onyekuru (Galatasaray, Turkey) da Peter Olayinka (Slavia Praha, Czech Republic) da Terem Moffi (Lorient, France) da Paul Onuachu (KRC Genk, Belgium) da Michael Olise (Reading, England) da kuma Adekunle Adeleke (Abia Warriors).

Source: BBC