Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Majalisar Dattawan Najeriya na son a ɗaure duk wanda ya biya kuɗin fansa shekara 15 a gidan yari

 113394828 Gettyimages 1149349367 594x594 Ahmed Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya

Thu, 20 May 2021 Source: BBC

Majalisar Dattawa a Najeriya na son a haramta biya da karɓar kuɗin fansa domin kuɓutar duk wani da aka yi garkuwa da shi.

Haka kuma majalisar ta nemi a yanke wa duk wanda aka kama ya biya ko ya karɓi kuɗin fansa hukuncin ɗaurin shekara 15 a gidan yari.

Sanata Ezenwa Francis Onyewuchi ne ya gabatar da kudirin na 2021 mai taken 'magance ayyukan ta'addanci kuma sanarwar ofishin shugaban majalisar dattawan ya fitar ta ce kudirin yanzu ya tsallake karatu na biyu.

Idan kudurin ya zama doka, hukuncin biyan kuɗin fansa za a iya aiki da shi a ko wanne lokaci.

Source: BBC