Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Mozambique: Yadda aka yi wa ɗan da na haifa yankan rago a gabana

 117589213 4600c827 882f 4337 9350 64c04dab797d Save the Children ta ce ana yi wa yaran da basu haura shekara goma sha daya ba yankan rago

Tue, 16 Mar 2021 Source: BBC

Kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa Save the Children ta ce ana yi wa yaran da basu haura shekara goma sha daya ba yankan rago a lardin Cabo Delgado da ke arewacin Mozambique.

Lardin na fama da tashin hankalin kungiyoyin masu dauke da makamai tun shekarar 2017, wanda ya haifar da rikicin jin kai.

Kungiyar ta ce ta jima tana magana da iyalan da aka raba da matsugunansu, kuma sun bata labarin mummunan yanayin tashin hankali da yankin ke ciki.

Wata mata ta bayyana yadda take kallo, lokacin da aka yi wa danta mai shekara sha biyu a duniya yankan rago, kwanaki kadan bayan da wasu masu dauke da makamai suka kashe danta mai shekaru 11.

An kuma kai hari a ƙauyensu, Rikicin da yankin nan Cabo Delgado ke ciki dai ya raba kusan mutane dubu 700 da gidajensu.

An kuma kashe fiye da mutane dubu biyu da dari shida.

Lardin mai arzikin iskar gas na fama da tashin hankalin da ake alakantawa da 'yan bindiga masu alaka da kungiyar masu rajin kishin Islama, wadanda suka mamaye kauyuka da garuruwa tun shekara ta 2017.

Babban tasirin da hare haren kungiyoyin ya haifar ga yankin na arewacin Mozambique na da matukar girman gaske.

Da yawa daga cikin dubunnan daruruwan mutanen da suka tserewa gidajensu sun gudu ne a cikin kwale-kwale, wasu daga cikinsu kuwa sun kife a teku, lamarin da ya haifar da mutuwar mutane dama.

Source: BBC