Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Rahoton Bankin Duniya: Nijar ta ƙere ƙasashen Afirka 10 a ɓunƙasar tattalin arziki

 117585401 Mediaitem117585400 Shugaban Jamhuriyyar Nijar mai barin gado Mahamadou Issoufou

Tue, 16 Mar 2021 Source: BBC

Nijar ta samu ɓunkasar tattalin arziki inda ta kere wasu ƙasashen Afrika a cewar wani rahoton Bankin Duniya.

Alƙalumman rahoton sun nuna cewa Nijar ta tashi daga matsayin ƙasa ta ƙarshe da ta fi talauci a duniya inda yanzu ta sha gaban ci gaban tattalin arzikin kasashe 10 ciki har da Saliyo

Rahoton ya ce ma'aunin tattalin arzikin ƙasar (GDP per capita) ya kai dalar Amurka 555 a 2019 adadin kuɗin da ɗan Nijar ke rayuwa a shekara.

Yanzu Saliyo ce ƙasa mafi talauci a nahiyar Afirka mai ma'aunin tattalin arziki dala 505, adadin da kowane ɗan ƙasar ke rayuwa a shekara.

Rahoton ya ce ci gaban ya faru ne sakamakon sabbin sauye-sauyen da aka yi a ƙasar mai yawan al'umma miliyan 24 tsakanin 2012 zuwa 2019.

"Babban ci gaban Nijar ya samo asali ne sakamakon sauye-sauyen da aka aiwatar, musamman ta fuskar shugabanci na gari da inganta yanayin kasuwanci," in ji rahoton na Bankin Duniya.

Wannan ne ya sa a cewar rahoton Nijar ta haura daga matsayi na 173 a 2012 zuwa matsayi na 132 a 2020, inda yanzu take bin Najeriya da ke matsayi na 131.

Rahoton ya kuma ce Nijar ta samun ci gaba sosai fiye da kasashe kamar Angola (da ke matsayi na 177, kuma daya daga cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a yankin kudu da hamadar Sahara, saboda yawan man da take hakowa), ko Habasha, wacce ta sauka daga matsayi na 111 zuwa 159.

Sai dai rahoton ya ce akwai babban ƙalubale ga ƙasar na ɗorewar ci gaban tattalin arzikin.

Me ya haifar da ci gaban?



Kamar yadda rahoton ya bayyana an inganta yanayin kasuwanci a ƙasar a shekarun baya-baya nan

Kuma masanin tattalin arzikin ƙasar Dr Soli Abdourahamane ya ce an samu ƙaruwar tattalin arzikin ne ta ɓunkasar fitar da kayyaki waje musamman fannin man fetur da kayan noma.

"Shekaru biyar ba a samu yunwa ba, an samu ci gaba wajen harakar abinci - wanda ke tasiri ga ci gaban tattalin arziki," in ji masanin.

Ya kuma ƙara da cewa Nijar ta karbo rancen miliyoyin kuɗi da aka yi ayyukan gine-ginen hanyoyi waɗanda kuma suna cikin ƙididdiga da Bankin duniya ya yi la'akari wajen bayyana matsayin ƙasar a fannin tattalin arziki.

Ra'ayi ya sha bamban

Sai dai yayin da masana kan fannin tattalin ariki ke cewa tabbas an samu ci gaba wasu masu rajin kare haƙƙin dan adam a kasar na ganin ba wani ci gaba da aka samu ganin yadda al'umma ke cikin mawuyacin hali.

Wasu na ganin ya kamata mutane su bambanta ci gaban tattalin arziki da ci gaban jin dadin rayuwa na dan adam - kuma a cewar Dr Soli Abdourahamane ci gaba sakamako ne na kuɗi da ke ƙaruwa a tsakanin yan ƙasa.

"Shi ya sa kowane lokaci aka ce Nijar ta samu ci gaba a fannin tattlin arziki yan kasar sai su dinga cece-kuce na cewa ba wani ci gaba da aka samu."

Masu fafutika kamar Nassirou Seidou sun danganta rahoton a matsayin wata tatsuniya ga ƴan Nijar.

Suna ganin babu tattalin arzikin da ya wuce a kula da ci gaban ilimi kuma gwamnati ta rarraba arzikin kasa talaka ya ji a jikinsa.

"Abin da talakan Nijar yake ci ki a yau ba yadda zai yarda cewa an samu ci gaba," " in ji Nassirou Seidou na ƙungiyar muryar talaka.

Amma masu goyon bayan gwamnatin Nijar kamar Surajo Isa ya ce wannan madogara ce ta miƙewar Nijar

A cewarsa shugaba Mohamadou Issoufou ya shinfida yadda Nijar za ta miƙe kumahar ta fara tasowa - "ya cika sharuɗɗan gina tubalin ci gaban ƙasa."

Gwamnatin ƙasar a nata bangaren ta ce jajircewarta ne ya kai ga samun nasara wannan ci gaban saɓanin abin da shugabannin baya suka kasa yi.

Source: BBC