Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

An yi gumurzu tsakanin sojoji da mayaƙan Boko Haram a hanyar Maiduguri

 117487325 Sojojinnajeriya Wasu rahotanni sun ce an kashe yan Boko Haram da dama

Tue, 9 Mar 2021 Source: BBC

An yi arangama tsakanin sojojin Najeriya da mayaƙan Boko Haram a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri inda shaidu suka ce sun ga mutum biyu na ci da wuta a gefen titi.

Bayanai na cewa lamarin ya auku ne ranar Lahadi da safe, a tsakanin garuruwan Jakana da Mainok da Beneshiekh, inda ƴan Boko Haram suka yi yunƙurin kutsawa wani sansanin soji, sai dai sojojin da taimakon yan uwansu na sama sun yi nasarar daƙile aniyar tasu.

Wasu rahotanni sun ce an kashe yan Boko Haram da dama a yayin musayar, kana an lalata motoci da makamai, amma babu bayanin ko an kashe wasu daga cikin sojojin.

Lamarin haifar da tsayawar ababen hawa dake tahowa daga Damaturu, da zummar shiga Maiduguri.

Wani direba da ya isa wajen da fasinjojinsa jim kadan bayan faruwar lamarin ya shaidawa BBC cewa da idonsa, ya ga mutum biyu na ci da wuta lokacin da suka isa wajen.

"Na bar Benishek, muna kan gaba kan cewa za mu wuce, amma akwai motocin da suka riga ni shiga sakamakon ba a buɗe hanya da ni ba na zo, dai dai inda aka yi abun zuwan da muka yi munga mutum biyu na ci da wuta, da kuma tarkacen yayi haka."

BBC ta tuntuɓi Daraktan watsa labaran rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Muhammad Yarima, amma ya ce suna ƙoƙarin tattara bayanan abin da ya faru.

Haɗarin da ke tattare da bin hanyar

Duk matafiyin da ke kan hanyar zuwa Maiduguri, zuciyarsa kan fara bugawa da zarar ya isa Benishek, ka dangana da Mainok da Jakana saboda irin mugun haɗarin da ke tattare da wajen.

Ƴan Boko Haram kan fito shawagi lokaci zuwa lokaci, kuma suna tare fasinjoji su yi awon gaba da su, wasu lokutan su kashe wasu a wajen, duk kuwa da cewa akwai ɗumibin jami'an tsaro da aka jibe a wannan hanya.

"Yanzu ta kai ta kawo idan suka fito kan jami'an tsaro suke yi, duk lokacin da suka yi ɓarin wuta da jami'an tsaro suka kore su, sai kuma su dawo su tare mutanen da ke wucewa," inji wani direba da ke bin hanyar.

Ya ƙara da cewa yadda suke yi shine: "Za su kasu kashi uku, na farko ba za su fito maka ba sai na tsakiya, idan kace za ka wuce su ka gudu sai na gaba su buɗe maka wuta, in kuwa ka ce za ka koma da baya ka gudu, nan ma sai na baya su nemi ranka kai tsaye, idan ka tsaya a tsakiya ne za su tsayar da kai, su yi maka tambayoyi in sun ga dama su barka ka wuce, in kuma ba haka ba su tafi da kai" inji shi.

Jihar Borno wadda ke fama da matsalar tsaro na ci gaba da fama da hare haren ƙungiyar Boko Haram, domin daf da kammala wannan labari mun samu labarin cewa sun yi yi artabu da sojoji a ƙaramar hukumar Abadam, kuma wata majiya ta shaidawa BBC cewa 'yan Boko Haram ɗin ne suka yiwa sojojin kwantan ɓauna.

Source: BBC