Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Mutane 137 aka kashe a Nijar - Gwamnati

 117670864 63df46fe 5bcc 4cf7 8177 C1db01984311 Shugaban Jamhuriyyar Nijar mai barin gado Mahamadou Issoufou

Tue, 23 Mar 2021 Source: BBC

Gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki na kasa baki daya na tsawon kwana uku da za a fara Talata, sakamakon wasu hare-hare da mayaka da ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai kan wasu kauyuka uku a jihar Tahoua, ranar Lahadi inda suka kashe mutane 137.

Hukumomin Nijar din sun sanar da makokin ne, tare da tabbatar da yawan mutanen da maharan suka hallaka a jerin hare-haren da suka kai a kauyukan da ke kan iyaka da kasar Mali da Burkina Faso da yammacin Lahadi.

Kafin sanarwar da hukumomin na Nijar suka fitar an yi ta bayar da alkaluma na yawan wadanda 'yan bindigar suka hallaka, zuwa kamar mutum 40, amma kuma da wannan sanarwar ta hukuma, ta tabbata cewa, mutanen sun wuce haka nesa ba kusa ba.

Wasu bayanai da BBC ta samu sun bayyana cewa maharan sun bude wuta ne a tarukan jama'a.

An kai hare-haren ne cikin kauyuka uku da ke yankin Tilia a jihar ta Tahuoa, wadanda ke iyaka da wani bangare na kasar Mali, yayin da kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da Mohamed Bazoun a matsayin zababben shugaban kasar.

An kuma kai sauran hare-haren wasu kauyuka biyu da ake kira Bakorat da Intazayene sai kuma bakin wata rijiya da masu kiwo ke shayar da dabbobinsu da ake kira Wirssanate.

An yi dauiki ba dadi tsakanin jami'an tsaro da maharan, wadanda daga baya suka gudu zuwa yankin iyakar Mali.

Nijar dai na fuskantar munanan hare-haren da ba ta saba gani ba a baya bayan nan, daga masu ikirarin jihadi, da kan kai farmaki a kan kauyuka da ke warwatse, ta hanyar amfani da Babura da motocin a-kori-kura galibi a yankuna na kan iyaka.

Ko a makon da ya gabata ma mayakan sun kai irin wadannan hare-hare a bangaren kasar Mali inda suka kashe sojojin kasar talatin da uku.

Nijar na daga cikin kasashen da suka yi hadaka, wadanda Faransa ke marawa baya a yankin Sahel, gamayyar da ake kira G5, wadda ke yaki da masu gwagwarmaya da sunan jihadi.

Akwai dai tawagar sojoji dubu daya da dari biyu da kasar Chadi ta bayar karo, dakarun da ake dauka mafiya karfi a yankin, domin tallafawa a yaki da barazanar masu tayar da kayar bayan.

Source: BBC