Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

'Yan bindiga sun sace ɗaliban firamare a Kaduna

 97722711 De89dee6 A373 4371 8c58 A9d3791f8291 Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da sace ɗaliban firame da malamansu a jihar

Mon, 15 Mar 2021 Source: BBC

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da sace ɗaliban firame da malamansu a jihar.

An sace ɗaliban ne a makarantar firamare ta Rema da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna, Samuel Aruwan, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa.

Sai dai ya zuwa yanzu hukumomi ba su bayyana adadin mutanen da aka sace ba daga makarantar.

Akwai ƙarin bayani nan gaba kaɗan...

Source: BBC