Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Har yanzu Neymar na jinya ba zai buga wa PSG wasa da Lille ba

 117600402 Neymarjunior Dan kwallon Paris St Germain Neymar Junior

Mer., 17 Mars 2021 Source: BBC

Neymar ba zai buga wa Paris St Germain karawar da za ta yi da Lille ranar Laraba a gasar kofin kalubalen Faransa ba.

Sai dai koci Mauricio Pochettino na fatan Angel Di Maria da kuma Marquinhos, wadanda barayi suka shigar musu gida a karshen mako, za su iya taka leda ranar Larabar.

Har yanzu dan kwallon Brazil bai gama murmurewa ba daga raunin da ya yi ranar 10 ga watan Fabrairu a fafatawa da Caen.

Tun farko PSG ta sanar cewar dan wasan zai yi jinyar mako hudu, amma Pochetino ya fada ranar Talata cewar yana fatan Neymar, mai shekara 29 zai buga wa kungiyar karawar da za ta yi da Lyon ranar Lahadi a Lique 1.

Tun farko an sa ran Neymar zai buga wa PSG wasa na biyu a Champions League karawar zagaye na biyu a Faransa da Barcelona, amma bai yi fafatawar ba.

Haka kuma PSG za ta yi wasan na ranar Lahadi ba tare da Pablo Sarabia ba, sakamakon jinya a karawar da za ta yi a gida a gasar ta Faransa.

Source: BBC