Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Yusuf Buhari 'zai auri Zarah Nasir Ado Bayero bayan sallah'

 117700874 Untitleddesign 3.png Hoton Yusuf Buhari tare da na Zarah Nasir Ado Bayero

Thu, 25 Mar 2021 Source: BBC

Yusuf Buhari, ɗa ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai auri Zarah Nasir Ado Bayero, 'yar gidan Sarkin Bichi, bayan sallah mai zuwa.

Wata majiya mai kusanci da fadar masarautar Bichi ta tabbatar wa BBC cewa ɓangarorin biyu sun haɗu sun tattauna kan soyayyar da ke tsakanin matasan biyu.

Kazalika majiyar, wadda ba ta so a ambaci sunata, ta ce ɓangaren shugaban Najeriya ne ya tafi wurin iyalan marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero domin neman auren Zarah Nasir Bayero.

"Ɓangaron biyu sun amince tare da tsayar da lokacin bikin zuwa bayan sallah, ta yiwu bayan sallar azumi ko kuma layya," in ji majiyar tamu.

Sai dai majiyar ba ta amsa tambayar BBC kan ko an kai kuɗin gaisuwar iyaye ko na na-gani-ina-so ba kamar yadda yake bisa al'ada.

Wasu majiyoyi sun ce matasan biyu sun haɗu da juna ne a ƙasar Ingila inda Yusuf ya kammala karatunsa na digiri yayin da ita kuma Zarah har yanzu tana ci gaba da nata karatun.

Tun da fari, jaridar Daily Nigeria da ake wallafawa a intanet, ta ruwaito cewa Yusuf zai auri Zarah Bayero nan da watanni kaɗan masu zuwa tana mai cewa tuni shiri ya yi nisa game da bikin.

Ta bayyana cewa an so a ɗaura auren tun watannin da suka gabata amma hakan bai yiwuwa ba saboda mahaifiyar Yusuf, Aisha Buhari, tana birnin Dubai, inda ta kwashe watanni da dama kafin ta koma Najeriya.

A watan Fabrairun 2018, fadar shugaban Najeriya ta ƙaryata labarin da ke cewa ɗan shugaban ƙasar Yusuf Buhari ya rasu.

Wasu shafukan intanet ne suka wallafa labarin da ke cewa dan gidan shugaban ƙasar ya rasu sakamakon raunukan da ya ji bayan hatsarin da ya yi a kan wani babur na alfarma a watan Disambar 2017 a Abuja.

A watan Maris ya komo Najeriya kuma tun daga lokacin ba a jin ɗuriyarsa sosai.

Yusuf ne ɗan Aisha Buhari na uku da zai yi aure tun da Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa a shekarar 2015.

Source: BBC