Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Najeriya : Yadda yajin aiki ya tsayar da al'amura cik!

 117879092 Mediaitem117879091 Shugaba Muhammadu Buhari

Fri, 9 Apr 2021 Source: BBC

Yajin aiki a Najeriya na barazanar durƙusar da fannoni da dama dake da matuƙar muhimmanci ga rayuwar 'yan ƙsar, kama daga kan fannonin da suka shafi shari'a da na ilimi, da uwa uba lafiya.

A halin da ake ciki ƙungiyar ma'aikatan kotuna, da ta malaman kwalejojin fasaha da kuma takwararsu ta likitoci masu neman ƙwarewa sun shiga yajin aikin sai baba ta gani, inda suka yi barazanar ci gaba da yajin aiki har sai gwamnatin tarayya ta biya musu buƙatunsu.

Ita dai gwamnatin na kukan cewa bata da kudin da za ta iya basu, saboda yadda tasirin annobar korona ya gurgunta tattalin arzikin ƙasar.

Likitocin masu neman kwarewa sun shiga yajin aiki ne tun farkon watan nan, suna neman hukumomi su kyautata yanayin aikinsu da kuma biyansu alawus-alawus da sauran hakkokinsu da suka maƙale.

Mataimakin sakataren ƙungiyar ma'aikatan kotunan Najeriya kuwa Sa'idu Magaji Karkarku ya shaidawa BBC cewa rashin samun yancin bangarenne ya tilasta musu shiga wannan yajin aiki, sannan akwai hukuncin kotu da ya tursasawa gwamnonin jihohi bawa bangaren cin gashin kai, sai dai duk da haka ba a daraja wannan hukunci.

Al'amura sun tsaya cik !

Ga marasa lafiyar dake kwance a asibitocin gwamnati, dole ne su jira har a kammala wannan yajin aiki kafin a ci gaba da kula da lafiyarsu, abin da ya sa tuni suka shiga wani hali.

Akwai rahotannin cewa marasa lafiya sun fara shiga halin ni 'yasu a jihohin kada da dama saboda wannan yanjin aiki da likitoci masu neman kwarewa suka shiga a Najeriyar.

A wasu jihohin arewa kamar jihar Kano, marasa lafiya na yin cikar kwari a shagunan sayar da magunguna wato kyamis-kyamis domin duba lafiyarsu, ko da kuwa cutarsu ta wuce zuwa nan, duka dai domin samun kulawa.

''Yawancin wadanda suke zuwa wajena masu hawan jini ne, kai har da wani mai ciwon suga da ya zo wajena fah'' inji wani mai kyamis yayin zantawa da BBC.

Shima wani mara lafiya da aka kai asibiti ranga ranga a jihar ta Kano domin duba lafiyarsa, ya shaidawa BBC cewa haka suka ƙare jiransu a asibiti ba tare da an kula su ba, don haka sai suka tafi wani kyamis don karbar magani.

Ba wannan ne farau ba

Yajin aiki a Najeriya dai a iya cewa ya zama ruwan dare, da wahala a shiga wata shekara a ƙareta ba tare da ka ji wani bangare ya shiga yajin aiki ba, walau dai saboda zargin gwamnati da nuna halin ko in kula ga tsarin tafiyar da aiki ko kuma rashin biyan hakkoki.

Ko da a bara, kungiyar malaman jamio'in Najeriya wato ASUU ta shafe fiye da shekara guda cir !, tana yajin aiki, kafin daga bisani annobar korona ta ƙara dagula al'amura, lamarin sa ya sa a shekarar babu ko da dalibi guda da aka yaye da sunan kammala karatu a jami'oin gwamnati.

Su dai kungiyoyin kwadago sun yi imanin cewa babu wani yare da gwamnatin Najeriya ke ji da ya wuce shiga yajin aiki., don haka suma suna yi ne kawai don sun fahimci cewa hanyar da za su iya bi kenan don ganin an biya musu bukatunssu.

Dangane da wannan yajin aiki na yanzu dai bayanai na cewa ko da an janye, to sauran rina a kaba, kasancewar akwai batun karin kudin man fetur da na lantar da kungiyar kwadago ta NLC ta nuna rashin amincewa da su, wadda kuma da yiwuwar nan gaba su shiga yajin aikin, sai dai masu suka na ganin laifi gwamnati ne a wannan lamari, ko da yake hukumomi na cewa suna tattaunawa da 'yan kwadagon don lalubo bakin zaren.

Source: BBC