Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Gerard Pique ya kara cin karo da koma baya

 117385517 Gerardpiquegetty Gerard Pique ya yi rauni a kafarsa ta hagu.

Thu, 4 Mar 2021 Source: BBC

Kungiyar Barcelona ta sanar da cewar mai tsaron bayanta, Gerard Pique ya yi rauni a kafarsa ta hagu.

Sai dai ba a fayyace lokacin da Pique zai kammala jinya ba, domin ya koma fagen taka leda, illa dai kungiyar ta ce likitoci za su ci gaba da auna girman raunin da ya yi.

Pique ya yi raunin ne a Copa del Rey da Barcelona ta kai karawar karshe, bayan da ta doke Seville 3-0 ranar Laraba, kenan ta yi nasara da ci 3-2 gida da waje.

Bayan da mai tsaron bayan ya yi raunin, likitoci sun duba lafiyarsa a gefen fili, daga baya ya koma karawar da aka tashi da shi sumul.

Mai shekara 34, bai dade da ci gaba da buga wa Barcelona tamaula ba a bana, bayan jinyar wata uku a wasa da Atletico Madrid a La Liga cikin watan Nuwamba.

Pigue ne ya ci wa Barcelona kwallo na biyu a Nou Camp ranar Laraba da wasan ya kai karin lokaci, wadda ta kara na uku ta kuma kai fafatawar karshe a Copa del Rey na bana.

Source: BBC