Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Ƙarfin rundunonin tsaron ƙasashe 10 da suka fi yawan jama'a a duniya

 117759501 378639a7 Ad5f 433e 989f 2bf8d1d9c8f0 Hoton sojoji

Mer., 31 Mars 2021 Source: BBC

Tun bayan da jagoran APC a Najeriya Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya yi kira da a ɗauki matasa miliyan 50 aikin soja, domin shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi yankunan ƙasar baki ɗaya mutane da dama ke yin tsokaci.

Kodayake daga bisani ya ce ya yi subutar baki ne game da batun yana mai cewa matasa miliyan biyar yake nufi, amma duk da haka 'yan Najeriya sun yi ta tsokaci game da kalaman nasa.

Masu sharhi irin su Dr Kabiru Adamu na kamafinin Beacon Consulting da ke nazarin tsaro a Najeriya da yankin Sahel ya ce babu yadda za a yi kasa irin Najeriya, wadda yawan al'ummar bai dara na kasashe irin su China da Indiya ba ta tara sojojin da suka kai miliyan biyar ballantana miliyan 50.

Ya jaddada cewa su ma masu yawan al'ummar ba su yi haka ba, saboda adadin ya saɓa wa hankali.

"Ita kanta China da tafi yawan jama'a a duniya sojojinta miliyan biyu ne da motsi, yayin da Indiya da ke biye mata ke da sojoji miliyan daya da dubu dari hudu, don haka wannan maganar ta Tinubu ta fi gaban hankali," in ji shi.

Bola Tinubu dai ya ba da shawarar ce yayin taron taya shi murnar zagayowar haihuwarsa da aka saba gudanarwa duk shekara, wanda a wannan karon aka yi a jihar Kano ranar Litinin.

BBC ta yi duba kan yawan jami'an tsaron ƙasashen duniya 10 suka fi yawan al'umma da suka haɗa da Najeriya. Mun yi amfani da bayanan shekarar 2021 na shafin Ƙungiyar Global Fire Power GFP, mai bin diddigin ƙarfin tsaron ƙasashen duniya.

Yawan dakarun tsaro a wannan muƙala na nufin yawan jami'an dukkan hukumomin tsaro na ƙasashen.

Haka shi ma ƙiyasin yawan jama'ar da bayanan shafin GFP ɗin muka yi amfani.

China

Ita ce ƙasar da ta fi yawan jama'a a duniya inda take da mutum biliyan ɗaya da miliyan ɗari huɗu da talatin da tara da dubu ɗari uku da ashirin da uku da ɗari bakwai da saba'in da shida (1,439,323,776).

GFP ya ce yawan dakarun tsaron China gaba ɗaya ya kai miliyan uku da dubu ɗari uku da hamsin da biyar (3,355,000). Shafin ya ce China ce ta uku mafi ƙarfin dakarun tsaro a duniya, duba da ƙarfin ba yawan jami'an ba.

Indiya

Indiya ce ƙasa ta biyiu mafi yawan al'umma a duniya da mtum biliyan ɗaya da miliyan ɗari uku da ashirin da shida da dubu casa'in da uku da ɗari biyu da arba'in da bakwai (1,326,093,247).

Yawan dakarun rundunonin tsaron Indiya kuma sun kai miliyan biyar da dubu ɗari da ashirin da bakwai 5,127,000. Ita ce ta hudu mafi ƙarfin dakarun tsaro a duniya, duba da ƙarfin ba yawan jami'an ba.

Amurka

Ƙasa ta uku mafi yawan al'umma a duniya inda take da mutum miliyan ɗari uku da talatin da biyu da dubu ɗari shida da talatin da tara da ɗari da biyu 332,639,102.

Amurka ita ce ƙasa ta farko mafi ƙarfin dakarun tsaro a duniya amma yawan dakarun tsaronta duka miliyan biyu da dubu ɗari biyu da arba'in da biyar da ɗari biyar ne 2,245,500.

Indonesiya

Ƙasa ta huɗu mafi yawan jama'a ita ce Indonesiya inda take da mutum 267,026366.

Yawan jami'an tsaronta ya kai miliyan ɗaya da dubu tamanin 1,080,000. Ita ce ƙasa ta 16 a jerin mafi ƙarfin dakarun tsaro.

Pakistan

Yawan jama'r Pakistan ya kai miliyan ɗari biyu da ashirin da uku, da dubu ɗari biyar da ɗari shida da talatin da shida 223,500,636, abin da ya sa ta zama ta biyar a mafi yawan mutane a duniya.

Yawan dakarun tsaron ƙasar ya kai 1,704,000. Shafin GFP ya sanya Pakistan a matsayin ƙasa ta 10 daga cikin 140 mafi ƙarfin dakarun tsaro.

Najeriya

Najeriya na da yawan al'umma har miliyan ɗari biyu da sha huɗu da dubu ashirin da takwas da ɗari uku da biyu 214,028,302. Hakan ya sa ta zama ta shida a jerin ƙasashen da suka fi yawan jama'a.

Yawan dakarun hukumomin tsaronta ya kai dubu ɗari biyu 200,000. Kuma ita ce ta 35 a mafi karfin dakarun tsaro.

Brazil

Brazil ce ƙasa ta bakwai mafi yawan jama'a a duniya da mutum miliyan biyu da sha ɗaya da dubu ɗari bakwai da sha biyar da ɗari tara da saba'in da uku 211,715,973.

Yawan dakarun tsaronta kuwa miliyan biyu ne da dubu saba'in da bakwai da ɗari biyar 2,074,500. Ita ce ta tara a jerin ƙsashen da suka fi ƙarfin dakarun tsaro.

Bangladesh

Bangladesh ce ta takwas a mafi yawan jama'a da miliyan ɗari da sittin da biyu da ɗari shida da hamsin da ɗari takwas da hamsin da uku 162,650,853.

Yawan dakarun rundunonin tsaronta ya kai miliyan bakwai da dubu huɗu 7,004,000. Ita ce ta 45 a jerin ƙasashen da suka fi ƙarfin dakarun tsaro.

Rasha

Rasha ce ta tara a mafi yawan jama'a da mutum miliyan ɗari da arba'in da ɗaya da 141,722,205. Yawan dakarun hukumomin tsaronta ya kai miliyan uku da dubu ɗari biyar da sittin da tara 3,569,000.

Ita ce ta biyu a mafi ƙarfindakarun tsaro bayan Amurka.

Mexico

Yawan al'ummar Mexico ya kai miliyan ɗari da ashirin da takwas da dubu ɗari shida da arba'in da tara da ɗari biyar da sittin da biyar 128,649,565.

Yawan dakarun rundunonin tsaronta ya kai dubu ɗari huɗu da goma sha bakwai 417,000. Ita ce ta 46 a jerin ƙasashen da suka fi ƙarfin dakarun tsaro.

Source: BBC