Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Rikicin Chadi: Ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a yankunan kasar

 118430750 87b5b840 009e 45d1 9921 80dc03f850cd Sabon gwamnati ta haramta zanga-zangar da gamayyar ƴan adawa da ƙungiyoyin fararen hula

Tue, 11 May 2021 Source: BBC

Ƴan sanda a Chadi sun harba hayaki mai sa ƙwalla domin tarwatsa masu zanga-zanga, wadanda suka bijerewa dokar da gwamnatin sojin ƙasar ta sanya ta hana zanga-zanga.

A wata ranar Juma'a ne sojojin da suka karɓe mulki bayan mutuwar shugaba Idriss Deby suka haramta zanga-zangar da gamayyar ƴan adawa da ƙungiyoyin fararen hula suka kira.

Rahotanni sun ce ƴan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar a N'Djamena.

Masu zanga-zangar sun fito saman tituna wasunsu suna ƙone tutar Faransa da ta yi wa Chadi mulkin mallaka.

Suna adawa da Faransa mai goyon bayan gwamnatin Idriss Deby kuma wadda suke zargin tana goyon bayan sojojin da suka ƙwace mulki bayan mutuwar shugaban.

Shugaban Fraansa Emmanuel Macron ya nuna goyon baaynsa ga wannan gwamnati, ya kuma halarci jana'iuzar marigayi tsohon shugaban kasar.

A ranar 20 ga Afrilu sojojin Chadi suka sanar da mutuwar Idriss Deby tare da naɗa ɗansa Mahamar Deby a matsayin wanda ya gaje shi.

Tun lokacin da zanga-zanga ta ɓarke, kuma bayanai sun ce sama da mutum 600 aka kama.

Mahamat Idriss Deby ya yi alƙawalin gudanar da zaɓe cikin watanni 18.

Source: BBC