Twitter: Zabar Ghana a matsayin hedikwatar kamfanin a Afrika ya ba da mamaki

 118175999 Gettyimages 1224552677 976549.png Twitternta zabe Ghana a matsayin hedikwatar kamfanin a Afrika

Tue, 27 Apr 2021 Source: BBC

Matakin Twitter na zabar Ghana a matsayin inda zai gina hedikwatarsa a yankin yammacin Afrika ya bai wa kasashe da dama mamaki, ya kuma janyo muhawara a fadin nahiyar.

Amma ga kamfanin, matakin na da alaka da yadda Ghana ke ba da damar "bayyana ra'ayi ba tare da tsangwama ba da kuma yadda mutane ke samun intanet ba tare da wahala ba".

Haka kuma samar da hedikwatar zai taimaka wajen gina kasuwanci ba tare da shinge ba - da habbaka kasuwanci da kuma zirga-zirga tsakanin kasashen nahiyar - wanda hakan zai tabbatar da Ghana a matsayin wata kasa da aka bude hanya da ita.

Ghana na kara zama "wata duniyar da ake iya tattaunawa kan batutuwa masu zafi kuma na ilimi da suka shafi nahiyar Afrika a kullum," in ji Twitter.

Nan da nan Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya kara watsa wannan labari na Twitter a shafinsa, yana cewa wannan mafarar "kyakkyawar alaka" kenan da kuma habbakar fasaha a Ghana.

"Ba karamin jin dadinmu ba ne mu bude ofishin kuma mu fara kasuwanci da Ghana."


Har yanzu wasu shugabannin kamfanoni ba su ce komai ba saboda girgizar da suka yi kan batun.

"A Afrika kasashen da aka fi dauka a inda fasaha ta fi karbuwa su ne, Masar da Najeriya da Afrika Ta Kudu da kuma Kenya," in ji wata kwararriya a fannin fasaha 'yar Kenya.

A cewarta, Kenya na da duk abin da ake so da fasaha za ta iya samun wurin zama musamman in ana maganar karfin intanet kuma muhallin zai wa kamfanin dadi.

"Dan haka ba karamin zabi mai kyau suka yi ba, amma dai zamansu a Ghana nasara ce ga nahiyar baki daya."

'Shugabanci na gari'

Ta wata fuskar kuma, wani kwararre a fannin fasaha dan asalin Najeriya Femi Longe ya ce daukar Ghana shi ne zabi mafi nagarta.

"Akwai duk abin da ake so na samun riba a kasuwanci a Najeriya amma maganar gaskiya ta fara zama wuri mai wuyar sha'ani ta fuskar kasuwanci. Ghana na kokari wajen samar da yanayi da zai ja hankalin mutane daga ketare su shiga kasar."

Ya yi aiki a kasashen biyu da fasaha ke kara karbuwa a cikinsu, a Najeriya ya yi aiki a Legas, a matsayin shugaban wani kamfanin fasaha na Kenya - wata kasa da ita ma fasaha ke da wurin zama a cikinta.

A ganinsa, shugaban Ghana ya matukar taka rawa wajen matakin da Twitter ya dauka.

"In ka dubi Kenya da Ghana da Najeriya ta fuskar daidaiton siyasa da kuma shugabanci na gari za ka ga kasa daya ta sha bamban a cikinsu.

"Idan kamfani yana ganin gwamnati na da wasu tsare-tsare da za su taimaka masa wajen habbaka, to zai zabi Ghana. An fi samun wasu abubuwa cikin ruwan sanyi a Ghana wadda ba ta da nisa da Najeriya, don haka za ka iya samun duk wata ribar kasuwanci a Najeriya daga cikin Ghana.

'Ana shan wuya a kasuwanci' a Najeriya

Koma-bayan da Najeriya ke fuskanta ya zama wani batun tattaunawa tsakanin masu kasuwanci tun bayan sanarwar da Twitter ya fitar.

Ministan yada labarai na Najeriya Lai Muhammed ya zargi kafafen yada labarai na kasar kan yawan fitar da labarai marasa dadin ji da suke yi a kodayaushe yana cewa: "Wannan ne abin da zai rika faruwa lokacin da kuke muzanta kasarku."


Akwai misalan kasuwancin da suke fuskantar koma-baya a Najeriya, daga ciki akwai hana harkokin sufuri da aka yi a Legas na kamfanonin Gokada da ORide da kuma Max.ng a 2020, duka na kamfanonin kasashen waje ne kuma an kaddamar da su ne domin bukatarsu da ake da ita.


'Yan Ghana na fatan tattalin arzikin kasar zai habaka saboda kafa kamfanin Twitter - sai dai suna neman a dauki mutanensu a matsayin ma'aikata.

"Za mu zuba ido muga ni in za su ba da gurbin aiki domin a samu su dauki wani kaso na mutanen Ghana a ofishin," in ji Regina Honu wata shugabar makarantar koyon kwamfuta a Accra.

"Kamfanoni na kara zuwa za ka ga 'yan kasar da ke zaune a waje na dawowa kuma sai ka ga 'yan wasu kasashen Afrika da yawa sun zo neman aiki a Ghana. Su ma dole su zo su nuna tasu kwarewar."

Cibiyar da take koyarwa na daya daga cikin cibiyoyi da suke haskakawa a Ghana kuma suke fitar da matasa masu hazaka.

George Appiah, shi ne babban darakta na cibiyar fahasa da ke Kumasi kuma ya ce a 2012 gwamnati ba ta mayar da hankali ba kan lamarin fasaha.

"Amma yanzu muna da gwamnatin da take da sha'awa kan fannin kuma mun fara ganin rawar da fannin zai iya takawa."

'Damar bai wa sabbin abubuwa habbaka'

Wani wanda muryarsa ta yi kaurin suna kuma daya daga cikin masu kamfanoni a Ghana Herman Chinery-Hesse ya ce kamfanonin gida na kara mutuwa yayin da na waje ke kara samun wurin zama.

Yana daya daga cikin shugaban kamfanoni na yammacin Afrika da suke samar da manhajoji. Ya ce yana tsammanin ganin ci gaban kamfanonin cikin gida sama da na waje.

"Ina 'yan Ghana ma'abota Twitter? An bai wa kananan kamfanoni damar su zama kamar Twitter?

Duk wannan sukar da ya yi, amma ya ce ya yi amannar za a samu tururuwar mutane daga kasashen ketare da za su zo neman aiki.

Hakan dai na nufin Ghana za ta koma cibiyar habaka sabbin kirkire-kirkire.

Source: BBC
Articles Similaires: