Culture

Actualités

Sport

Business

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Ronaldo zai ja ragamar Portugal a gasar Turai ta bana

 118593716 Ronaldoportugal Cristiano Ronaldo

Lun., 24 Mai 2021 Source: BBC

Cristiano Ronaldo zai ja ragamar tawagar Portugal a gasar cin kofin nahiyar Turai a bana, bayan da koci Fernando Santos ya bayyana 'yan wasan da za su wakilci kasar.

Ronaldo wanda ya lashe Italian Cup a makon nan ya ci wa Juventus kwallo 100 shi ne kyaftin din tawagar da zai taka leda tare da dan wasan Manchester City, Bernardo Silva da kuma Bruno Fernandes na Manchester United.

Sauran 'yan wasan masu cin kwallaye a Portugal din sun hada da Joao Felix na Atletico Madrid da dan kwallon Liverpool, Diogo Jota.

Wani dan wasan mai zura kwallaye a raga da ke cikin tawagar shi ne Andre Silva wanda yake kan gaba a ci wa Eintracht Frankfurt kwallaye a Bundesliga.

Tun a bara ya kamata a buga gasar cin kofin nahiyar Turai wadda cutar korona ta sa aka dage wasannin zuwa bana da za a fara 11 ga watan Yuni.

Portugal mai rike da kofin nahiyar Turai tana rukuni na shida da ya hada da Faransa da Jamus da kuma Hungary.

Tawagar za ta buga wasan sada zumunta da Spaniya ranar 4 ga watan Yuni, kwana biyar tsakani ta fafata da Israel.

'Yan wasan tawagar kwallon kafa Portugal:

Masu tsaron raga: Anthony Lopes (Olympique Lyon) da Rui Patricio (Wolves) da kuma Rui Silva (Granada)

Masu tsaron baya: Joao Cancelo (Manchester City) da Nelson Semedo (Wolves) da Jose Fonte (Lille) da Pepe (Porto) da Ruben Dias (Manchester City) da Nuno Mendes (Sporting) da kuma Raphael Guerreiro (Borussia Dortmund)

Masu buga tsakiya: Danilo Pereira (Paris St Germain) da Joao Palhinha (Sporting) da Ruben Neves (Wolves) da Bruno Fernandes (Manchester United) da Joao Moutinho (Wolves) da Renato Sanches (Lille) da Sergio Oliveira (Porto) da kuma William Carvalho (Real Betis)

Masu cin kwallaye: Pedro Goncalves (Sporting) da Andre Silva (Eintracht Frankfurt) da Bernardo Silva (Manchester City) da Cristiano Ronaldo (Juventus) da Diogo Jota (Liverpool) da Goncalo Guedes (Valencia) da Joao Felix (Atletico Madrid) da kuma Rafa Silva (Benfica).

Source: BBC