Culture

Actualités

Sport

Business

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Caraboa Cup: Man City ta lashe kofi na hudu a jere na takwas jumulla

 118197449 Gettyimages 1134735497 Pep Guardiola kocin Manchester City

Sat, 1 May 2021 Source: BBC

Manchester City ta lashe Caraboa Cup na bana, bayan da ta yi nasarar doke Tottenham da ci 1-0 ranar Lahadi a Wembley.

Sauran minti takwas a tashi daga wasan ne City ta ci kwallo ta hannun Aymeric Laporte.

An buga wasan karshen da 'yan kallo sama da dubu bakwai a gwajin da ake yi ko magoya baya za su iya shiga stadiya nan gaba.

Sabon koci, Ryan Mason ne ya ja ragamar Tottenham wadda ta sallami Jose Mourinho ranar Lahadi, bayan da kungiyar ke mataki na bakwai a kan teburin Premier.

Wannan ne karo na hudu a jere da City ta dauki kofin na takwas jumulla, inda ta yi kan-kan-kan da Liverpool wadda itama keda takwas a tarihi.

City wadda Chelsea ta fitar da ita a FA Cup tana ta daya a kan teburin Premier League da tazarar maki 10 tsakaninta da Manchester United ta biyu.

Haka kuma City za ta je Faransa ranar Laraba domin buga wasan daf da karshe a karon farko a Champions League da Paris St Germain.

Source: BBC