Culture

Actualités

Sport

Business

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

SOKAPU: Muna bukatar a raba Jihar Kaduna gida biyu

Nasir El Rufai Nasir El-rufa'i, Gwamnan jihar Kaduna

Sam., 29 Mai 2021 Source: BBC

Wasu al'ummomi a Najeriya daga bangarori daban-daban na ta shirye-shiryen gabatar da kudurorinsu a game da shirin kawo gyara ga kundin tsarin mulkin kasar.

A jahar kaduna maganar ta yi nisa, wasu daga cikin al'ummomin kudancin jihar na nuna neman a ba su nasu bangaren a yayin da wasu daga cikin yan kudancin ke cewa har yanzu basu da cancantar a ce sun balle daga Kaduna.

To sai dai an gamu kuma an rabu. Kungiya Fulani makiyyaya ta Mi Yati Allah da ita ma ke cikin yankin na kudancin Kaduna ta ce ba da yawunta ba a cikin wannan lamari.

Johnathan Osake shugaban kungiyar yan kudancin Kaduna wato SOKAPU ya yi wa BBC karin bayani game da hujarsu:

Latsa lasifikar da ke sama domin saurarenrahoton da wakilin BBC Abdou Halilou ya hada.

"Kudancin Kaduna da bangaren arewacinsa an dade ana rashin zaman lafiya. Al'adunmu da daban, kuma mun san cewa idan aka raba jihar, kowa yaje yana cin gashin kansa, gaskiya zai kawo zaman lafiya."

Sai dai an gamu kuma an rabu. Kungiyar Fulani makiyyaya ta Mi Yati Allah da ita ma ke cikin yankin na kudancin Kaduna ta ce ba da yawunta ba a cikin wannan lamari.

Ibrahim Bayero shi ne mai magana da yawun kungiyar ta Mi Yetti Allah:

"Abin da su ka rubuta mu ba ma tare da su. A matsayinmu na Fulanin Kudanci, ba su neme mu ba, saboda haka Jihar Gurara da su ke nema, mu ba mu goyi bayan haka ba. Idan za a kirkito jiha sai an dubi tattalin arzikin yankin, al'ummar nan da su ka rubuta wannan takardardun, gaba dayansu ba sa iya tara haraji."

Source: BBC