Culture

Actualités

Sport

Business

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

Prince Philip: Yadda Yarima ya ziyarci kasashe 143

 96722916 Mediaitem96722915 Yarima Philip tare da Sarauniyar Ingila

Lun., 12 Avril 2021 Source: BBC

A matsayinsa na basaraken Birtaniyan da ya fi dadewa a ayyukan agaji, Mai martaba Duke na Edimburgh ya shafe shekaru da dama yana raka sarauniya a rangadin da take yi zuwa kasashe rainon Ingila, da ma wasu kasashen na daban.

Sannan kuma shi a karan kansa Yarima Philip, ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashen waje har sau 637. Daga cikin wannan adadi, tafiya 229 ya yi tane zuwa kasashe 67 na renon Ingila.

Sannan sauran tafiye-tafiye 408 ya yi su ne zuwa sauran kasashe.

Bayan rasuwar sarki George VI wanda hakan ya sa Gimbiya Elizabeth ta zama sarauniya, sun yi tafiya ita da angonta a shekarar 1952.

Daga nan ne Mai martaba Duke ya ci gaba da tafiye-tafiyensa na ziyarar aiki har zuwa kasashe 143.

Jim kadan da fara mulkin sarauniya, sai ma'auratan suka fara wata ziyara ta wata-shida zuwa kasashe renon Ingila, daga watan Nuwambar 1953 zuwa watan Mayun 1954, inda suka ziyarci kasashe 12 a mota, wasu a jirgin-ruwa, wasu kuma a jirgin sama.

A shekarar 1956 Mai martaba Duke ya yi rangadi na wata-hudu da nufin fadada kasashe renon Ingila zuwa yankin Trans-Antarctic.

Tafiya ce ta bazata, don haka Birtaniya ce kasa ta farko da ta shiga yankin Antarctic, kuma Yarima ne basarake na farko da ya ratsa yankin.

Yarima ya fara yin tafiyar ne a jirgin ruwa da Mumbasa, inda ya yi tafiyar kimanin mil 40,000.

Ya bi ta kasar Seychelles da Ceylon, da Malaya, da New Guinea har ya isa Australia, inda a nan ne ya kaddamar da wasan Olympic na 1956 a birnin Melbourne na New Zealand da Antarctica da Tsibirin Falkland da Georgia ta Kudu da Tsibirin Gough da Tristan da Cunha da St Helena da Ascension da kuma kasar Gambiya.

Yarima ya rika daukar hotunan tsuntsaye a lokacin da yake tafiye-tafiye, kuma ya adana su da kyau, inda daga baya ya tattara su a cikin littafi guda daya da ya sanya wa suna ''Tsuntsaye daga Birtaniya ''wato '' Birds form Britannia'' a Turance. An kuma buga littafin a shekarar 1962.

Wani labari da aka buga a Mujallar Times a watan Yunin 1957, an jero hotunan wasu manyan namun daji cikin wasu hotuna dari da aka bajewa jama'a su kalla, a wajen taron bajekolin kayayyakin tarihi a matsayin tsarabar tafiyar Mai martaba Duke.

A taron bajekolin, har da hotuna guda 47 da wani Mista Edward Seago ya Zana, wanda ya hau jirgin ruwan Yarima a lokacin da yake tafiya zuwa kasar Australia.

A ranar kirsimeti ta shekarar 1956, maganganun da Yarima Philip ya yi a lokacin da yake tafiya a cikin jirgin ruwa, kuma ya aika da su Birtaniya, su aka fara sawa, kafin sarauniya ta yi wa al'ummar kasar jawabin murnar kirsimeti daga fadarta ta Sandringham dake Norfolk.

A cikin jawabin da sarauniya ta yi ta bayyana cewa; ''Muna zuba idon ganin lokacin da za mu sake kasancewa tare ni da mijina.''

Sai dai an yi cece-kuce a kan wannan tafiya ta Yarima.

Jaridun Birtaniya sun yi ta yin tambayoyi a kan tsawon lokaci da Yarima ya dauka a wajen rangadinsa, ba tare da amaryarsa ba.

A lokacin da yake daf da kammala rangadin, sarauniya ta hau jirgin sama domin ta je ta hadu da mijinta a kasar Portugal, kwanaki biyu kafin ya fara rangadi a kasar.

A lokacin bikinsu na cika shekaru 25 da aure, a shekarar 1977, Sarauniya da Mijinta Yarima Philip sun yi wata tafiya zuwa kasashe rainon Ingila, sun ziyarci birnin Papua na New Guinea da birnin West Indies.

A gida Birtaniya kuwa, Sarauniya da Yarima sun ziyarci larduna guda 36 a fadin kasar, duk a cikin shekararsu ta bikin cika shekaru 25 da aure.

A shekarar 1979, ma'auratan sun shiga kasashen yankin Gulf a jirgin ruwa, inda suka ziyarci kasashen Kuwaiti da Bahrain da Saudiyya da Qatar da Tarayyar Daular Larabawa da kuma Oman.

Shekaru uku bayan nan kuma suka yi tafiya zuwa yankin Pacific ta Kudu.

Yarima Philip ya ziyarci India sau uku. Daya daga cikin daukakar da Birtaniya ke da ita, ita ce ta samun 'yancinta da ta yi tun kafin sarauniya Elizabeth ta hau gadon mulki.

Mai martaba Duke ya fuskanci suka a shekarar 1997, bayan kasancewarsa Shugaban Kungiyar Kare Namun Daji na Farko da ya fara kashe zaki a kasar.

Ma'auratan sun kai ziyarar karshe zuwa kasar India a shekarar 1997, lokacin bikin cikarsu shekaru 50 da samun 'yancin kasar Indian.

Sai dai tafiyar ba ta yi dadi ba saboda kalaman da Sakataren Harkokin Birtaniya, Rabin Cook ya taba yi a kan yankin Kashmir, wanda hakan ya sa Firaministan kasar India ya bayyana Birtaniya a matsayin kasa ''mai Katsa-landan a harkokin wasu kasashe.''

Sarauniya ba ta taba ziyartar Isra'ila ba, amma a shekarar 1994 Yarima Philip ya zama Babban Basarake daga Birtaniya da ya fara ziyartar kasar.

Ya yi ziyara kasashe da dama na duniya ba tare da sarauniya ba, mafi yawan tafiye-tafiyen ya yi su ne lokacin da yake Shugabantar Kungiyar Kare Namun Daji, sai kuma tafiye-tafiye da ya rika yi a matsayin wakilin sarauniya domin halartar jana'izar manyan mutane a sassa daban-daban na duniya.

Ita ma Sarauniya ta yi tafiye-tafiye da dama bisa amincewar ofishin Kula da Harkokin Kasashen Waje, hakan ya kara nuna irin kakkyawar dangantaka ta Diplomasiyya tsakaninta da sauran kasashen duniya.

Kasashe uku ne kadai Sarauniya ta taba zuwa tare da mijinta a yankin Latin Amurka, inda suka ziyarci Brazil da Chile da Mexico.

Sai dai kuma shi Yarima Philip ya ziyarci kasar Argentina a 1962. Kuma rahotanni a wancan lokaci sun ruwaito cewa, shugaban kasar yana fuskantar bore, amma duk da haka ba a bari boren ya shafi karramar da aka shirya yi wa Mai martaba Duke ba.

A shekara ta 2002, lokacin bikin cika shekaru 50 na sarauniya a kan karagar mulki, Sarauniya da mai gidanta sun yi tafiyar kimanin mil 40,000 a fadin Birtaniya da wasu kasashen duniya, ciki har da Jamaica da New Zealand, inda a nan ne suka fara haduwa ido-da-ido da dan-majalisa na farko maza-mata a duniya.

A yayin tafiyar tasu dai, lokacin da suka isa Canada, sun ya da zango, inda har suka shiga cikin wasan kwallon gora da ake yi a cikin kankara, kuma a nan suka hadu da mutumin da ya zama zakara a gasar hawa tsauni ta duniya, wato Mista Bryan Adams.

Tun a cikin tafiye-tafiyen da suka yi na farko suka ziyarci kasar Australia a shekarar 1954.

Kuma sun koma kasar tare da wasu 'yan gidan sarautar Ingilan a tsakanin shekaru 60, bayan ziyararsu ta farko.

A shekarar 2006 sarauniya ta bude gasar wasanni ta kasashe renon Ingila, kuma daya daga cikin tafiyar da suka yi ta baya-bayan nan ita ce ta halartar taron shugabannin kasashe renon Ingila.

A shekara ta 2015, Sarauniya da mai gidanta sun ziyarci Tsibirin Malta a rangadinsu na kwana uku a tsibirin da dama can sun taba zama a cikinsa.

Sun hau kwale-kwale ne in da suka ratsa ta yankin Valletta wanda nan ne wurin da Sarki George VI ya yi sansani a shekarar 1943 domin nuna girmamawa ga tsofaffin 'yan mazan jiya na Birtaniya bisa jajircewarsu a kan abokan gaba a Yakin Duniya na Biyu.

Kuma da can sarauniya da mai gidan nata sun taba zama a yankin na Valletta lokacin farkon aurensu, daga shekarar 1949-1951 tun kafin sarauniya ta hau gadon mulki, sannan kuma shi ma Yarima Philip ya taba zama a yankin a matsayin sojan ruwa.

A shekara ta 2007, sarauniya da mai gidanta sun koma Tsibirin Mediterranean domin bikin murnar cikarsu shekaru 60 da aure.

Bayan shekaru masu yawa na tafiye-tafiye da Yarima Duke ya yi a duniya ya fahimci irin cigaba da wannan duniya ta samu ta fuskar fasaha.

Ya tabe cewa a shekara ta 2002 ''Duk mutumin da ya yi tafiye-tafiye irin wadanda muka yi zai yaba da cigaban da aka samu ta fuskar kera jirgin sama na alfarma kuma mai saukin kara, musamman ma idan ba bangaren fasinja gama-gari ka shiga ba, inda karar da ake ji ta fi yawa.''

Source: BBC