Menu

AU ta dakatar da Mali saboda juyin-mulkin sojoji

 118770571 1807c432 Ce02 4f12 A9ee 2f7a9425f964 Kanar Assimi Goïta ne ya shugabanci juyin mulki a Mali

Wed, 2 Jun 2021 Source: BBC

Kungiyar haɗin-kan Afirka wato AU, ta dakatar da Mali a matsayin mambanta a wani martani na juyin mulkin da sojoji suka aikata a makon da ya gabata a ƙasar. Sannan ta yi barazanar kakaba takunkumi idan ba a mayar da mulki karkashin gwamnatin farar-hula ba.

Wannan shi ne karo na biyu da tarayyar ke dakatar da Mali a cikin wata 9. Na farko shine a watan Agustan bara lokaci da sojoji suka kifar da gwamnati - sai dai ƙasar ta sake dawo wa cikin kungiyar bayan sanar da farar-hula a matsayin wanda zai jagoranci gwamnatin rikon kwarya zuwa lokacin sabon zabe.

Yanzu da aka sake kifar da gwamnatin da ke riko, Mali ta sake tsintar kanta cikin yanayi na wariya.

Kungiyar hadin-kan Afirka wato AU ta bukaci a tattauna mayar da mulki cikin sahihanci ga gwamnatin rikon, idan hakan ya gaza faruwa ta yi gargadin cewa ba za ta ba ta lokaci ba wajen kakabawa ƙasar takunkumi.

AU ta bukaci gwamnatin soji ta mutunta tsarin da aka aminta na rikon-kwaryar watannin 18 kafin a gudanar da zaben shugaban ƙasa a watan Fabarairu badi.

Matakin AU na zuwa ne kwana biyu bayan shugabannin kungiyar kasashen yammacin Afurka ECOWAS, sun dakatar da kasar Mali daga cikinsu.

Jagoran juyin mulkin Kanar Assimi Goita ya ayyana kan shi a matsayin shugaban riko, sannan ya halarci taron da ECOWAS ta yi a birnin Accra na kasar Ghana.

Shi ma shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya yi gargadin cewa ƙasarsa za ta janye dakarunta a Mali, idan har rikicin siyasa a ƙasar ya ƙara haifar da tsattsauran ra'ayin Islama.

Faransa wadda ke kan gaba wajen yaki da masu ikirarin jihadi na da sojoji 5,100 a Mali da ke yankin Sahel.

Shimfida

A ranar Litinin din makon da ya wuce ne Kanar Assimi Goita ya sake jagorantar juyin mulki a karo na biyu, tare da kama shugaban rikon Mali Bah Ndaw, da kuma Firai minista Moctar Ouane.

Wasu rahotanni sun ce ya dauki matakin ne saboda sauye-sauyen da aka yi a gwamnati da nada sabbin mukamai ba tare da an tuntube shi ba.

Tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Keita, Mali ta shiga halin rashin tabbas, farar hula ba su daina bore ba kan rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da kasar, tare kuma ta kiran lallai a sanya lokacin zabe domin maida kasar tafarkin dimukradiyya.

Source: BBC