Kakakin majalisar wakilai Najeriya, Femi Gbajabiamila, ya ce dole ne ƙasar ta sake nazarin manufofin ta na kasashen waje domin kare muradun ta na kasa ga al'ummar duniya da ke sauyawa.
Gbajabiamila ya nuna cewa kamata ya yi ƙasar ta fayyace tsare-tsaren manufarta ta hanyar shiga alaƙa da sauran ƙasashe don magance dumbin matsalolin da ke addabarta.
Kakakin ya fadi haka ne a wani taron tattaunawa kan nazarin manufofin kasashen waje na Najeriya a Abuja, taron na gudana ne tsakanin kwamitocin hulɗa da ƙasashen waje a majaisun tarayya da haɗin gwiwar ma'aikatar harkokin waje.
Ya ce tuni ya kamata a ce an yi nazari akan manufofin kasar, yana mai cewa abubuwa da yawa sun sauya tun daga shekarun 1960 lokacin da manufofin Najeriya kan harkokin kasashen waje suka soma aiki.
Shugaban ya ba da misali da matsalar sauyin yanayi da musayar kuɗaɗen jari cikin sauƙi da yaƙi da matsalar safarar kuɗaɗe don ayyukan ta'addanci da ci gaban ƙere-ƙere cikin hanzari a matsayin wasu sabbin ƙalubale da ke canza yadda duniya ke juyawa.
"Fasaha ta sauya yadda muke gudanar da kasuwanci kuma ta samar da dama ga miliyoyin mutane a fadin duniya. Haka ya sanya mu cikin hadari saboda fasahohin zamani da kayan aikin sun zama mahimman sassan rayuwarmu wadanda zaa iya amfani da su don cutar da mu''.
"Yan ta'adda, masu aikata laifi da kuma muggan 'yan wasa na dukkan fuskoki yanzu suna da damar samun kayan aikin da zai basu damar aiki cikin sauki tare da kaucewa hukumomin bincike.
Mista Gbajabiamila ya kara da cewa, "Yakamata manufofin kasashenmu na kasashen waje su bayyana ka'idojinmu na yin hulda da sauran kasashen duniya domin kowa ya tsira tare.
Shugaban kwamitin hulɗa da ƙasashen waje a majalisar wakilai Yusuf Buba Yakubu ya ce a tsakiyar shekarun 1980 an yi irin wannan kwaskwarima sai dai gwamnatin wancan lokaci ba ta yi amfani da ita ba, don haka suka taro masu ruwa da tsaki daga faɗin ƙasar a wannan lokaci.
Yusuf Yakubu ya ce duniya ta zama mai saurin canzawa da ke buƙatar wata bakandamiyar manufar hulɗa da ƙasashen waje daga Najeriya fiye da tsohuwar tata wadda ta fi mayar da kan 'yancin Afirka.
Ya ce irin wannan manufa jazaman ne ta ƙunshi aƙidoji da za su sa Nijeriya ta ninka ribar da take samu daga alaƙar da take ƙullawa da duk wani ɓangaren duniya ya Allah nahiyar asiya ne ko Afirka ko Turai ko kuma nahiyar Amurka.
Femi Gbajabiamila dai na fatan duk wata sabuwar hulɗa da ƙasashen waje da za a samar, ta fi mayar da hankali wajen shiga alaƙar da za ta taimaki ƙasar wajen shawo kan manyan-manyan matsalolinta na taɓarɓarewar tsaro da samar ayyukan yi, wadanda suka fi yi wa Najeriya barazana a wannan zamani.