Tun a makon da ya gabata ne ake yada wani bidiyo da ke nuna yadda sararin samaniyar Masallacin Ka'aba da ke Saudiyya ya rikide ya zama ja jazur.
Bidiyon wanda ya yaɗu kamar wutar daji musamman a shafin sada zumunta na Whatsapp, ya sa mutane da dama sun yi amanna cewa "Alamu ne na Tashin Alƙiyama."
A saƙon da ke tafe da bidiyon an rubuta cewa: ... "wannan ne abin da ya faru a Saudiyya a yau, iska mai tafe da guguwar rairayin hamada mai launin ja ta rufe sararin samaniyar Masallacin Harami da kewaye."
Ganin yadda mutane da dama da ke ci gaba da yaɗa saƙon sun yi amannar cewa alamu ne na tashin Alƙiyama ya sa BBC ta bi diddigin bidiyon.
Mun tuntuɓi hukumomin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya wato Haramain Sharifain ta shafin Tuwita, kuma sun yi bayani kan yadda al'amarin ya kasance.
Haramain Sharifain ya ce irin wannan al'amari ya sha faruwa ba ma a Masallacin Ka'aba ba kawai har ma da ɗaukacin sauran yankunan ƙasar.
Lamarin kan faru ne a duk lokacin da iska ta taso daga Hamadar Sahara mai ɗauke da ƙura.
A duk lokacin da irin wannan iska ta taso ta kan turnuƙe sararin samaniyar yankunan ƙasar ta inda ko tafin hannu ba a iya gani.
Hukumar Haramain Sharifain ta sake cewa a irin waɗannan lokuta mutane kan ɗauki bidiyo su yi ta yaɗawa.
"Mun yi ƙoƙarin nemo muku ainihin bidiyon da ake yaɗawar amma mun kaso gano shi, amma dai an sha samun lokuta da irin hakan kan faru a Saudiyya," a cewar saƙon da Haramain Sharifain ya aiko wa BBC Hausa ta Tuwita.
Sakon ya ci gaba da cewa: "Hakan yawanci kan faru ne a yayin da iskar mai ɗauke da matsananciyar guguwa ta taso daga Sahara ta lullube yankin sai launin samaniyar ya zama ja ko ruwan goro."
Lokaci na baya-bayan nan da aka yi irin wannan shi ne ranar 13 ga watan Maris ɗin nan inda mafi yawan yankunan ƙasar ciki har da Masallacin Ka'aba suka shaidi hakan.
Sannan hukumomin Haramain Sharifain sun ce a shekarar da ta gabata ma sau biyu irin wannan guguwa mai ƙura ta turnuƙe sararin samaniyar ƙasar.
Wani bidiyo da shi ma aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna yadda iskar ta dinga kayar da fitilun kan titi.
Wata mazauniyar birnin Damam ta shaida wa BBC cewa a ranar da abin ya faru ko tafin hannunta ba a iya gani kuma dole aka dakatar da duk wata zirga-zirga.