Menu

Abin da ya sa ƴan Najeriya da ke tsare a Saudiyya suka yi yajin cin abinci

 113556966 Dd54e991 4f47 4796 85fb 52c47f254d79 Sarkin Saudiyya a wata taro da shugaba Buhari

Thu, 4 Mar 2021 Source: BBC

Wasu 'yan Najeriya da ke tsare a gidajen yarin Saudiyya sun koka kan mawuyacin halin da suke ciki tsawon watanni tun bayan kama su, da nufin izo ƙeyarsu zuwa gida.

Sun dai yi iƙirarin cewa sun kai ɗaruruwa a gidajen yarin da ke Jeddah da Riyadh, cikinsu har da mata da ƙananan yara.

Mutanen da ke tsaren sun faɗa wa BBC cewa har yajin cin abinci sun yi don sanar da mahukunta halin da suke ciki, amma a duk lokacin da suka tuntuɓa sai a faɗa musu cewa aikin kwaso su yana hannun ofishin jakadancin Najeriya.

A cewar ɗaya daga cikinsu "aƙalla mun kai kimanin wata huɗu zuwa wata shida kuma aƙalla mata za su kai ɗari uku da wani abu, tsakaninmu da su akwai tazara kuma maganar yajin aikin cin abinci tabbas mun yi".

Shi ma wani da ya kasance cikin wannan hali ya bayyana cewa sun shiga wani hali mawuyaci har ma a cikinsu a kwai tsofaffi in da ya ce "wani ma tsohon da ƙyar yake tashi".

Sun dai ce abin da kawai suke nema a yanzu shi ne gwamnati ta kai musu ɗauki domin fitar da su daga ƙangin da suke ciki ta hanyar mayar da su gida.

Ga muryoyin 'yan Najeriyar da ke tsare a Saudiyyan:

Source: BBC