Kasashen Afrika ba su shiga cikin jerin wadanda suke neman China ta sauya yadda take tafiyar da lamarin 'yan kabilar Uyghur ba wadanda yawancin su Musulmai ne da ke rayuwa a yankin arewa maso yammacin yankin Xinjiang.
A baya-bayan nan wasu jami'an diflomasiyya daga Afrika sun halarci wani taro a Beijing kuma sun yi magana kan manufofin China a yankin.
An yi amannar akwai akalla 'yan kabilar Uyghur da ake tsare da su a wani sansani a Xinjiang. Kuma kan haka China na shan suka da zargi kan yadda take sanya su aikin karfi da yadda take azabtar da su da kisan kiyashin da take musu, sai dai ta sha musanta hakan.
Gwamnatin China ta kare matsayarta ta tsare sun da take yi a sansanonin, tana cewa wajen koya sana'o'i ne da kuma kara ilimantarwa, sannan suna sauya tunanin 'yan tada kayar ba da masu ra'ayin rikau kan addini.
"Da dama daga kasashen yamma na zuzuta wannan halin da ake ciki a Xijiang wanda hakan kamar wani kaddamar da hari ne kan China domin dai su cimma wata boyayyiyar manufarsu," in ji wakilin Burkina Faso a China Adama Compaoré, an ruwaito ya fadi hakan ne a wata makala da ya gabatar a watan Maris kan yadda wakilan Afrika ke kallon China. Sudan da Congo-Brazzavile sun halarci taron.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch (HRW) ta ce taron wani mataki ne na nuna halin ko in kula da kasashen Afrika ke yi kan matsalar da ta dami duniya.
"Zai iya yiwuwa hakan an yi ne saboda diplomasiyya, amma gwamnatocin Afrika da suka yi shiru kan wannan lamari ya ci karo da abin da duniya ta damu a kan shi," in ji Carine Kaneza Nantulya jami'ar wayar da kai a kungiyar a yankin Afrika.
Sauyin aka samu cikin dogon lokaci ne?
Amma wani jami'i da ke aiki da Global Governance Institute a Brussels Ejeviome Otobo ya ce, akwai fahimtar juna tsakanin China da kasashen Afrika a wurare uku: Kare hakkin dan adam da muradin tattalin arziki da kuma rashin yin katsalandan kan al'amuran cikin gida.
Wani babban abu da Afrika ta yi wa China game da akalarsu ta gwamman shekaru shi ne, rawar da kasashen suka taka wajen dawo da ita cikin MDD lokacin da take tsaka da rikici da Amurka a 1970.
"Tun daga nan dangantakar kara karfi take yi" Cliff Mboya wani dan kasar Kenya da ke zaune a China kuma mai shrhi kan al'amura ya shaida wa BBC.
Sama da shekara 30 China ta mayar da shi kamar wata al'ada ministan harkokin wajenta na zuwa Afrika a farkon ko wacce sabuwar shekara - wannan ba wata manuniya kan yadda China ke daukan Afrika da mahimmanci, hakan kuma na da tasiri ga Afrikawan,"
Babu mamaki hakan ba zai burge matasan nahiyar ba - domin ci gaban Amurka da salonsa ya fi birge su, kamar yadda binciken Afrobarometer ya nuna.
Amma manyan yankin da kuma shugabannin gwamnatoci abin daban yake a wurinsu - kuma matakin da suka dauka wajen dogaro da China domin samar da ci gaba cikin shekaru 20 baya - ya sauya yankin ta hanyar samun manyan tituna masu kyau da gadoji da layin dogo da filayen jirgi ga kuma intanet kuma hakan ya sa nahiyar ta kara rike China da mahimmanci.
"Kasashen yamma za su iya mana haka? ya kara da cewa zai yi wuya su zuba makudan kudi a nahiyar kamar haka.
Diflomasiyyar da ke cikin rigakafi
Tun da annobar korona, aka-akai ake ganin tutar kasar China a filayen jirgin saman nahiyar wanda hakan ke nuna yadda take kawo taimakon kayan kariya da kuma allurar rigakafin da ta samar a kusa.
Ya zuwa yanzu rabon rigakafin ya isa kasashe 13 a nahiyar Afrika, wadanda ko dai sun saya ne ko kuma an basu a matsayin tallafi
Idan aka kwatanta babu wani taimako da Amurka da Burtaniya suka kawo wa yankin kai tsaye sai dai ta karkashin shirin Covax - wanda shi ma taimako ne daga China. Covax ta raba rigakafi miliyan 18 ya zuwa yanzu a kasashe 41 na Afrika.
Samar da allurar Covid-19 na daya daga cikin hanyoyin kame kananan kasashe da manyan kasashen duniya ke tsere a akai.
A watan Maris sakataren harkokin wajen Burtaniya Dominic Raab ya shawraci kasashen da suka ci gaba da su jira a samu wani rigakafin maimakon amfani da na China da Rasha.
Sabon Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yana kallon yanayin a matsayin koma baya, a kusan nan ya shaida wa daliban nahiyar Afrika cewa "Ba mu ce kuzaba ba tsakanin Amurka da China, amma muna baku shawarar ku tambayi abubuwa masu mahimmanci yawan bayanin da kuka samu zai ba ku damar zabi."
Manyan kasashen yamma sun san ba za su hada kansu da China ba idan ana maganar bayar da aron kudi da kuma ayyukan raya kasa - ba su da abin da za su iya yiwa kasashen da ke amfana da taimakon China ko kuma su yi gogayya da Beijing din. Maimakon haka sai dai su yi kiran a samar da tsarin dimokradiyya da kuma yaki da cin hanci da rashawa.
Dalilin haka, da yiwuwar anan kusa ko wacce kasasr Afrika za ta so ta goyi bayan shugaban China a Hague kan yadda ake tafiyar da lamarin 'yan kabilar Uyghur - kamar yadda ya faru da Aung San Su Kyi a 2019, lokacin da take shugabantar Myanmar kuma tsohon ministan shari'a na Gambia ya shigar da ita kara kan yadda ake yi wa 'yan kabilar Rohingya musulmai marasa rinjaye.