BBC

Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

MenuAfrique
BBC

Man United ta yi wa Aston Villa gida da waje a bana

 118439041 Edisoncavani Sauran minti uku su tashi daga fafatawar Edinson Cavani ya ci na uku

Mon, 10 May 2021 Source: BBC

Manchester United ta ci gaba da zama ta biyu a teburin Premier League, bayan da ta doke Aston Villa da ci 3-1 a Villa Park ranar Lahadi.

Villa ce ta fara cin kwallo ta hannun Bertrand Traore a minti na 24 da fara tamaula, kuma haka suka je hutu Aston Vila da ci daya.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne United ta farke ta hannun Bruno Fernandes a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Minti hudu tsakani da United ta farke, sai ta kara na biyu ta hannun Mason Greenwood.

Sauran miki uku su tashi daga fafatawar Edinson Cavani ya ci na uku da ya tabbatar United ta samu maki uku a wasan.

Ko a wasan farko da suka buga a Premier League a bana cikin watan Janairu, United ce ta yi nasara da ci 2-1, kenan kungiyar Old Trafford ta doke Villa gida da waje a bana.

Haka kuma Traore shi ne ya ci wa Villa kwallo a Old Trafford, shima Fernandes ne ya zura kwallo na biyu a ragar Villa, bayan Anthony Martial da ya ci na farko.

Source: BBC