Menu

Afghanistan: Mun yi nasara kan Amurka a yaƙinmu da ita - Taliban

 118053515 Hajihekmat.png Shugaban Amurka wai zasu janye dukkan sojojin su a Afghanistan

Fri, 16 Apr 2021 Source: BBC

Tuki zuwa yankin da Taliban ke da iko da shi ba zai ɗauke ka dogon lokaci ba.

Baifi tafiyar minti 30 ba daga arewacin birnin Mazar-e-Sharif, za ka yi ta wuce wasu manyan ramuka a gefen titi da bam ya fasa, mun hadu da wanda ya sauke mu Haji Hekmat ɗan Taliban mai kular mata da gundumar Balkh.

Ya zo sanye da baƙin rawani, yana daya daga cikin tsaofaffin 'yan kungiyar wadanda suke cikinta tun 1990, lokacin da suke iko da mafi yawan yankunan kasar.

Taliban ta shirya nuna mana dakarunta. Sun jera dakarun a gefen tituna dauke da manyan makamai, wani na dauke da gurneti irin mai harbo jirgin saman nan, akwai makamin M4 wanda suka ƙwata a hannun dakarun Amurka.

Yankin Balkh na daya daga cikin yankuna masu kwanciyar hankali a kasar, amma yanzu ya koma mafi tashin hankali.

Baryalai, daya daga cikin kwamandojin Tabilan da ya yi fice saboda tsananinsa, ya nuna mana tsallaken titi inda ya ce, "Ga dakarun gwamnati can a kusa da babbar kasuwa, amma ba za su iya ƙarasowa nan ba. Wannan yankin na masu jihadi ne".

Irin wannan halin ake ciki a fadin Afghanistan: Gwamnati ce ke da iko da manyan biranen kasar, amma Taliban na zagaye da su ta ko ina, inda take mamaye da yankunan gefe-gefe na kasar.

Su 'yan bindigar suna ware yankunansu ne ta hanyar sanya shingen duba ababen hawa a manyan tituna. Aamir Sahib Ajmal, wanda shugaban hukumar leken asiri ne na Taliban ya ce suna neman mutanen da ke da alaƙa da gwamnati ne.

"Za mu kama su, mu kai su gidan yari," in ji shi. " Sai kuma mu miƙa su ga kotunmu su kuma su yanke musu hukunci."

Taliban na da yaƙinin za su samu nasara. Haji Hekmat ya yi ikirarin cewa, "Mun samu nasarar wannan yaƙin kuma Amurka ta sha kasa".

Hukuncin da shugaban Amurka Joe Biden ya dauka na jinkirta janye dakarun kasar har zuwa watan Satumba.

Hakan na nufin za su ci gaba da zama a kasar su wuce lokacin da aka fara sanyawa na farko wato 1 ga watan Mayu a bara, wannan ya janyo wata gagagrumar murna daga shugabannin siyasar kungiyar Taliban.

"A shirye muke don tunkarar komai," in ji Haji. Mun shirya domin tabbatar da zaman lafiya, kuma mun kintsa don yaƙi. A gefensa wani kwamanda ne a zaune: "Jihadi ibada ne. Kuma ibada abu ne da zaka riƙa yi ba tare da gajiya ba."

Sama da shekara guda, an yi ta fuskantar kwan-gaba-kwan-baya a jihadin Taliban". Sun daina kai hari kan dakarun kasashen waje saboda yarjejeniyar da suka sanya wa hannu tsakaninsu da Amurka, amma sun ci gaba da yaki da dakarun Afghanistan.

"Amma Haji Hekmat ya ce babu wani abun da zai ruɗa mutane a yaƙin da suke yi.

"Kawai muna bukatar gwamnatin Addinin Musulunci da za ta shugabanci kasar da Shari'a, za mu ci gaba da jihadinmu har sai sun miƙa wuya."

Ba maganar cewa Taliban za ta raba iko da shugabannin siyasar Afghanistan ba ne, magana ce ta cewa abin da shugabanninsu da ke Qatar suka ce a yi shi za a yi, in ji Haji.

Taliban ba sa daukar kansu a matsayin kungiyar 'yan tawaye, sai dai a matsayin gwamnati mai jiran gado.

Suna kiran kansu a matsayin "Majalisar Musulunci ta Afghanistan" sunan da suke amfani da shi lokacin da suke da iko a 1996 har zuwa lokacin da aka kifar da su bayan kai harin 9/11.

Lokacin da suke da iko a 1990 sun haramta wa 'ya'ya mata neman ilimi, amma yanzu sun ce suna ƙarfafa gwiwar yara su riƙa yi, duk da cewa akwai rahotonni a wasu yankunan ba a barin 'yan matan da suka balaga zuwa karatu.

Matukar za su sanya Hijabi ba mu da damuwa da karatunsu, yana da matakar mahimmanci a gare su, in ji Mawlawi Salahuddin, da ke lura da ma'aikatar ilimi ta Taliban.

Majiyar yankin sun shaida wa mana cewa 'yan Taliban sun sanya cire darasin zane-zane da na 'yan kasa daga manhajar karatu tare da maye gurbinsu da darussan addinin Musulunci.

Shin 'yan Taliban na tura 'ya'yansu mata makaranta?

"'Ya'yana mata kanana ne, amma idan suka girma zan sanya su a makarantar boko da Islamiyya, matukar suna bin tsarin Shar'ar musulunci na sanyawa mata hijiabi," in ji Salahuddin.

Gwamnati na biyan ma'aikata albashi, amma 'yan Taliban ke kula da hakan. Hakan ake yi a dukkan kasar.

Lamarin haka yake a wani asibiti da wata kungiyar agaji ke tafiyarwa. Taliban na amincewa mata ma'aikata su yi aiki, amma dole su samu namiji da ke jagorantarsu da daddare, ana kuma ware marasa lafiya maza da mata a wurare daban.

Ana samun bayanai akan abin da ya shafi tsarin iyali da takaita haihuwa. 'Yan Taliban suna son mu dinga musu kallon rahama. A lokacin da muka wuce ayarin 'yan mata sun taso daga makaranta, cikin farin ciki Haji Hekmat yake alfahari da abin da suke yi.

Amma duk da haka ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda Taliban ke kallon hakkin mata. Ƙungiyar ba ta da wakilai mata, a shekarar 1990 suka hana mata yin aikin da ba daga gida za a yi ba.

Wani mazaunin yankin da ya amince ya yi mana ƙarin haske, kan sharadin ba za mu fadi sunansa ba, ya ce Taliban suna da matukar tsauri fiye da tunaninmu, ba kamar yadda suka nuna a lokacin tattaunawarmu ba.

Ya bayyana cewa ana lakadawa ƙauyawa duka da sharara musu mari, matukar suka aske gemu ko gashin bakinsu, ko aka same su da sauraren kade-kade.

"Mutane ba su da zabi face su bi umarninsu," kamar yadda ya shaida wa BBC, ya kara da cewa: "ko a kan batun da bai taka kara ya karya ba sai su fusata su fara lakadawa mutane duka, don haka mutane a tsorace suke."

A lokacin da muke wuce ƙauyukan da ke gundumar Balkh, mun ga mata da yawa, kuma ba dukkansu ne suke sanye da Burqa ba, suna tafiya hankali kwance.

A wata kasuwar ƙauye kuma babu mace ko guda. Haji Hekmat ya kafe cewa ba a haramta wa mata zuwa kasuwar ba, amma ya amince a wasu gidajen masu tsattsauran ra'ayi ana hana mata zuwa kasuwa.

Duk inda muka sanya kafa, 'yan Taliban ne ke mana rakiya, yawancin mazauna ƙauyukan da muka zanta da su, sun nuna goyon baya ga kungiyar da gode musu kan yadda suka shawo kan matsalar aikata muggan laifuka tsakanin jama'a.

"Lokacin da gwamnati ke iko da ko ina, ana daure mutanenmu da neman na goro kafina sake su," kamar yadda daya daga cikin Taliban ya shaida mana.

"Mutanenmu sun wahala, amma a yanzu muna cikin farin ciki da walwala."

Source: BBC