Menu

'Allah yana fushi da mu': Al'umomin Uganda na fuskantar barazanar narkewar ƙankara

 117609327 79692e92 86f5 4e4e B222 C7725ed0ae28 Al'umomin Uganda na fuskantar barazanar narkewar ƙankara

Fri, 19 Mar 2021 Source: BBC

Ronah Masika na tuna lokacin da ta ga kankara na zagwanyewa daga saman tsaunukan Rwenzori, wani wuri da Hukumar Raya Al'adu Ta Duniya UNESCO ke dauka da muhimmanci, wanda ke tsakanin iyakar Uganda da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Duk lokacin da ta yi tafiya zuwa Kampala babban birnin Uganda daga garinsu Kasese idan tana kallon wajen tana ji kamar kar ta daina saboda abin sha'awarsa - kuma a kwanan nan hakan ya faru.

Amma yanzu fargabar kallon wurin take ma saboda zagwanyewar da kankarar ke yi.

Kuma ba wannan ne sauyin da aka samu ba kawai.

Masika na tuna yadda kakarta ta wajen uwa ke shuka wake ta rika ciyar da iyalanta da shi, kuma ba zai lalace ba har sai an kara shuka sabo lokacin roronsa ya yi.

"Ba a dauki wani dogon lokaci ba da hakan ke faruwa, za ka ga ni a wannan watan sannan ya dauke a watan gaba,"in ji Masika wacce ke shuka masara da wake da gyada da waken suya da makani da ayaba.

"A yau ni da sauran mutanen da muke noma ba ma iya samar da abin da za mu iya rike gidajenmu da shi, saboda ambaliyar ruwa da fari sun yi kaca-kaca da yankin, ko dai a samu fari mai yawa ko kuma ruwan da ya fi karfin kasarmu.

"Yana sa in ji ba dadi, duk lokacin da na tuna yadda 'ya'ya da jikokinmu za su rayu a wannan wuri mai hatsari a nan gaba."

Rikicewar yanayi

Sauyin yanayi na lalata duwatsun tsaunukan Rwenzori ta hanyoyi da dama.

Abin da aka fi gani a zahiri kankarar da ke kan tsaunin ita ma tana raguwa yanzu, ta ragu daga murabba'in kilomita 6.5 a shekarar 1906 zuwa kasa da murabba'in kilomita 1 a 2003, kuma za ta iya karewa nan da shekara 10 masu zuwa.

A 2012, an samu gobarar daji da ta cinye bishiyoyi da yawa, wadanda suke taimakawa ruwan ya shigo tsa tsakanin bishiyoyi.

Tun daga nan, al'ummar da suke rayuwa a kasan wurin ke fama da matsalar ambaliyar ruwa da ba su taba ganin irinta a baya ba.

A watan Mayun da ya gabata, wasu koramu biyar suka cika makil bayan wani ruwa da aka yi kamar da bakin kwarya. Ruwan ya rika kwararowa daga tsaunuka yana ruguje manyan gidaje da makarantu da shaguna ya yi awon gaba da wani kauye da ake kira Kalembe.

Kimanin gidaje 25,000 ne suka lalace, kuma ambaliyar ta shafi mutum 173,000.

Yayin da ilimin kimiyya ke kokarin neman musabbabin faruwar abin, mutane na amfani da al'adar Bakonzo domin lalubo dalilin faruwar abin, a amannarsu ubangiji ne ke fushi da mutane.

'Mazaunin kankara'

"Kabilun Bakonzo sun yi matukar amanna da kankara da ke kan tsaunuka da kuma ruwan da ke gangarowa," in ji Simon Musasizi shugaban wata kungiya mai kula da al'adu ta Uganda.

"Sun yi amannar cewa Ubangijinsu Kithasamba na rayuwa ne a cikin kankara, kuma wannan kankarar ce ke samar da wata nasara ga ubangijinsu."

Asalin sunan tsaunukan Rwenzori ya fara ne daga rwe nzururu, wanda ke nufin "fadar kankara" a yaren Bakonzo. A imanin da suka yi, akwai ubangiji 30 da ke rayuwa a tare da wasu albarkatun kasa da suke da su.

Amma sare bishiyoyi da karuwar yawan al'uma da amfani da bindiga da masu farauta ke yi suna tsorata mutane na daga cikin abin da ke lalata alakarsu da mutane.

A bara, wata ambaliya da aka samu ta yi awon gaba da fadar da ake zuwa a yi bauta a cikinta tun daga nan, shugabanin addinansu ba a iya zuwa su gabatar da abubuwansu na bauta.

Haduwar koramu da ke burge Bakonzo da kuma gudanar da abubuwan al'adunsu ya fuskanci koma baya saboda da cika da kasa da koramun suka yi.

A wani wurin kuma yawan ruwan ya karu, abin da ke janyo ambaliya kenan.

Lalata shuke-shuken daji ya sanya gabar koramun ta yi rauni a yankuna da yawa, nan da nan ruwa sai ya tsallako.

Al'adun da aka gada na fuskantar hadari

Al'umar Bakonzo sun kusa miliyan daya wadanda ke rayuwa a duka bakin iyakokin Uganda da na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, kuma al'adunsu da yawa sun bata saboda bayyanar addinin Musulunci da na Kirista.

Wannan barazanar da sauyin yanayi ya haifar na nuna a nan gaba za a iya rasa karin wasu al'adun masu muhimmanci.

"Sakamakon sauyin yanayin da ake fuskanta na karuwa musamman a yankin da ke da zafi, in ji Taylor, wani masanin kimiyyar kasa a kwalejin Landan.

"Ma'aunin zafi daya ko biyu a tsakiyar duniya yana da matukar tasiri kan sauyin yanayi da ruwa sama da irinsa a Landan ko Paris ko New York."

Fari ya zama wani ruwan dare a yankunan Amboseli da Serengeti na Tanzaniya da Kenya, kuma yana da tasiri a kan mutanen Maasai. Kankara kuma na raguwa sosai a dutsen Kenya da Kilimanjaro.

Neman mafitar da Bokonzo ke yi da kuma sauyin yanayin da ake samu daga ubangiji ya zama abin mamaki ga Masika wadda ta girma a wani karamin gida mabiya addini Musulunci.

"Lokacin da muka fara wannan aikin, jikina ya rika yi mani kaikayi. Amma duk lokacin da na ziyarci ruwa mai tsarki, ina tabbatarwa da sai na yi wanka da ruwan," in ji ta.

"Akwai zafi nan wurin, za ka ji zafi kamar ana kona ka. Daga nan sai ka karasa bakin ruwan gaban inda zafin ya yi yawa, ruwan sai kaji sanyi kamar an saka a kankara.

"Amma kana barin wurin, za ka ji wani dadi jikinka, kuma tun daga nan na daina jin kaikayi a jikina."

Source: BBC