Menu

An bada belin jagoran 'yan hammaya a Senegal

 117498658 Gettyimages 1126716056 Ousmane Sonko

Tue, 9 Mar 2021 Source: BBC

Wani alkali a Senegal ya tuhumi jagoran 'yan hammaya Ousmane Sonko da aikata fyade tare da bayar da shi beli, bayan an kwashe kwanaki ana mumunar zanga-zangar da ta yi sanadin kame shi a makon jiya.

Etienne Ndione, daya daga cikin lauyoyinsa ya ce "Zai koma gida. An sake shi ."

Ana zargin Mista Sonko, mai shekara 46, da cin zarafin wata mata da ke aiki a wani gidan gyaran gashi.

Ya ce shari'ar na da nasaba da siyasa don hana shi sake tsayawa takara a zaben 2024. Ya zo na uku a zaben 2019 da kashi 16% na kuri'un.

Masu zanga-zangar sun yi artabu da jami'an tsaro a wajen kotu a Dakar, babban birnin kasar, kafin a fara sauraren karar a ranar Litinin.

'Yan sanda sun girke motoci masu sulke a cikin garin sakamakon rikicin da aka kwashe kwanaki ana gwabzawa inda aka kashe akalla mutane takwas, ciki har da wani matashi a garin Diaobé da ke kudancin kasar - rikici mafi tsanani da kasar Senegal ta gani tsawon shekaru.

Har ila yau, an harba hayaki mai sa hawaye a kan masu zanga-zangar a tsakiyar Dakar a ranar Litinin, bayan da suka yi wa jami'ai ruwan duwatsu.

Mista Sonko yana da farin jini a tsakanin matasa 'yan Senegal, kuma wata kungiyar hammya da aka fi sani da Movement for the Defence of Democracy ta yi kira da a gudanar da zanga-zangar kwanaki uku, fara daga Litinin.

An kuma ba da umarnin rufe makarantu a babban birnin kasar tsawon mako guda sakamakon rikicin.

Masu goyon dan hammayar sun shewa sun a cewa a 'a saki Sonko ' a wajen kotu

A ranar Lahadi wani babban jami'in Senegal wanda aikinsa shi ne sasanta rikice-rikice, Alioune Badara Cissé, ya ce hukumomi "suna bukatar su tsaya su tattauna da matasanmu" kuma ya yi gargadin cewa "muna gab da shiga wani mataki na rikicin da baa taba ganin irinsa ba".

Source: BBC