Menu

An gano birni mai shekara 3,000 da 'ya yi ɓatan dabo' a Masar

 117894070 066654749 1 Masana sun ce birnin mai suna Aten shi ne tsohon abu mafi girma da aka taɓa ganowa a Masar

Sat, 10 Apr 2021 Source: BBC

An jinjina tare da yabon wani ƙoƙari na gano wani tsohon birni da ya shekara 3,000 wanda ƙasa ta rufe shi a Masar, a matsayin aikin ilimin binciken tarihi mai matuƙar muhimmanci da aka yi tun bayan gano kabarin Tutankhamun.

Fitaccen mai ilimin binciken tarihi Zahi Hawass ya sanar da gano "birnin da ya yi ɓatan dabon" a kusa da Luxor a ranar Alhamis.

Ya ce birnin mai suna Aten shi ne tsohon abu mafi girma da aka taɓa ganowa a Masar.

An gano birnin ne cikin makonni kaɗan da aka fara tono shi a watan Satumban 2020.

Ana alaƙanta daɗewar birnin da zamanin mulkin Sarki Amenhoteo na III, ɗaya daga cikin fir'aunonin Masar masu ƙarfin mulki, wanda ya yi mulki daga shekarar 1391 zuwa 1353 kafin haihuwar Annabi Isa.

Wasu fir'aunonin kamar Ay da Tutankhamun sun ci gaba da amfani da birnin, waɗanda wani masanin binciken tarihi na Birtaniya Howard Carter ya gano ƙaburburansu a Tsaunin Sarakuna a shekarar 1922.

Betsy Brian, wata farfesa kan ilimin tarihin Masar a Jami'ar John Hopkins da ke Baltimore a Amurka ya ce, "Gano wannan tsohon birni shi ne abu na biyu mafi muhimmanci a ilimin binciken tarihi tun bayan gano ƙabarin Tutankhamun."

Ta ce birnin "zai ba mu wata dama ta ganin abin da ba kasafai ake gani ba cikin rayuwar Masar ta baya" a lokacin da daular take cikin arziƙinta.

Haƙar ta bayyanar da wasu abubuwan tarihi masu yawa kamar kayan ƙawa na mata da tukwane masu launi da bulo din ƙasa masu tambarin Sarki Amenhotep III.

Tawagar ta fara haƙar ne a gaɓar yamma da kogin Luxor kusa da Tsaunin Sarakuna, mai nisan kilomita 500 daga kudancin Alƙahira.

A wata sanarwa Dr Hawass ya ce, "Cikin makonni, ga mamakin tawagar sai ga shi an fara ganin bulollukan gine-gine daga dukkan ɓangarorin."

"Abin da suka tono ɗin wani gagarumin birni ne da yake cikin yanayi mai kyau, kuma bangwayensa duk suna nan tsaf, sannan wasu an samu kayayyakin amfanin yau da kullum a wasu ɗakuna."

A yanzu bayan wata bakwai da fara tonon, an gano wurare da dama da ke kusa da birnin, da suka haɗa da gidan gashi, da wata gundumar gudanar da sha'anin mulki da kuma gidajen zama.

"Hukumomin ƙasashen waje da dama sun yi ta neman birnin amma ba su gano shi ba," a cewar Dr Hawass, tsohon ministan kayayyakin tarihi.

Ya ce ana ci gaba da tono kayayyakin tarihi a wajen kuma ana sa ran tawagarsa za ta tono ƙaburburan da ke cike da abubuwan tarihi.

Masar na son inganta ɓangaren kayayyakin tarihinta don farfado da harkar yawon buɗe ido a ƙasar.

A makon da ya gabata aka yi jerin gwanon gawarwakin tsoffin shugabannin Masar 22 a Alkahira inda za a sauya su zuwa wani sabon gidan adana kayan tarihi da ke kudancin birnin.

  • Za a nuna gawar Fir'auna da tsoffin sarakunan Masar
Source: BBC