Iran ta soma samar da karfen uranium, duk da gargadin da kasashen Yammacin duniya suka yi mata cewa yin hakan tamkar keta yarjejeniyar makamin nukiliya ce da aka rattabawa hannu a 2015.
Masu bincike na hukumar da ke sanya ido kan makamashi ta duniya sun tabbatar cewa kasar tana da 3.6g (0.1oz) na sinadarin a tasharta da ke Isfahan a makon jiya.
Iran ta ce tana gudanar da bincike kuma tana samar da karfen ne da zummar samar da fetur da masu bincike suke amfani da shi.
Sai dai ana iya amfani da karfen uranium wajen hada bom na nukiliya.
Iran ta dage cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne, amma ta yi watsi da yarjeniyoyi da dama game da kera makaman nukiliya a shekaru biyu da suka wuce.
Ta ce tana yin hakan ne domin martani ga jerin takunkuman karya tattalin arzikin da gwamnatin Amurka karkashin jagoranci Donald Trump ta sanya mata a 2018 lokacin da ya yi watsi da jarjejeniyar da aka kulla.
Mutumin da ya gaje shi, Joe Biden, ya ce dole ne Iran ta yi biyayya ga dukkan yarjejeniyar da aka kulla idan tana so ya janye mata takunkuman. Sai dai shugaban Addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce dole Amurka ta soma janye takunkuman da ta sanya mata kafin ita ma ta dakatar da abin da take yi.
Hukumar ta AEOI ta dage cewa ana samar da karfen uranium kacokan domin ayyukan zaman lafiya, tana mai cewa ba ta keta wata yarjejeniyar kasashen duniya kan kera makaman nukiliya ba.
Birtaniya, Faransa da Jamus - manyan kasashen duniya uku cikin biyar da har yanzu ke cikin yarjejeniyar nukiliya - sun ce sun yi "matukar damuwa" da jin sanarwar da Iran ta fitar kan batun.
Sun yi gargadin cewa: "Iran ba ta da wata hujja ta samar da karfen uranium. Samar da karfen uranium zai iya jawo da martani na soji."
A watan Disamba, majalisar dokokin Iran ta amince da wani kudurin doka da ya bukaci gwamnati kammala tashar kera makamin uranium da ke Isfahancikin watanni biyar.
'Yan majalisa masu tsattsauran ra'ayi sun gabatar da kudurin ne bayan kisan da Isra'ila ta yi wa wani masanin nukiliya Mohsen Fakhrizadeh a watan Nuwamba.