Menu

An samu mutumin da ya kamu da sabon nau'in murar tsuntsaye a China a karon farko

 118771285 Gettyimages 73225724 Akwai nau'ukan murar tsuntsaye daban-daban, inji masana

Thu, 3 Jun 2021 Source: BBC

An tabbatar wani dan kasar China mai shekara 41 ya zama mutum na farko da ya kamu da wani sabon nau'in murar tsuntsaye.

Jami'ai ba su bayar da cikakken bayani kan yadda mutumin ya kamu da nau'in na murar tsuntsaye ba amma ana ganin nau'in na H10N3 yana da wahala ya yadu tsakanin mutum da mutum.

Mutumin wanda ke zaune a lardin Jiangsu, wanda aka tabbatar ya kamu da nau'in na murar tsuntsaye a makon jiya, yanzu yana samun sauki kiuma ana shirin sallamarsa daga asibit.

Akwai nau'ukan murar tsuntsaye daban-daban kuma ba sabon abu ba ne idan mutanen da ke aiki a gidajen kiwon kaji da ma wasu tsuntsaye su kamu da cutar.

Bibiyar da aka yi wa mutanen da ya hadu da su ta nuna cea babu wanda ya kamu da sabon nau'in cutar.

Hukumar Lagfiya ta Beijing ta bayyana ranar Talata cewa an kwantar da mutumin mazaunin birnin Zhenjiang a asibiti ranar 28 ga watan Afrilu inda aka gano yana dauke da nau'in na H10N3 wata daya bayan haka.

"Ba a samu rahoton bullar nau'in na human H10N3 a jikin dan adam ba a dukkan fadin duniya. Wannan karon an samu yaduwar cutar daga dabba zuwa mutum wanda ba kasafai ake samun hakan ba, kuma babu yiwuwar za ta yadu sosai," a cewar shugaban Hukumar a hirarsa da jaridar Global Times.

Hukumar ta kara da cewa cutar murar tsuntsayen nau'in H10N3 ba a haifar da cutuka masu zafi a jikin dabbobi kuma da wahala ya yadu cikin gaggawa.

Hukumar Lafiya ta duniya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "a wannan lokaci, babu wata alama da ke nuna cewa za a samu yaduwar cutar daga mutum zuwa mutum".

A halin da ake ciki an samu barkewar cutar murar tsuntsaye nau'in H5N8 wadda ta yi sanadin kashe daruruwan dubban tsuntsaye a kasashen Turai da dama.

A watan Fabrairu, Russia ta bayar da rahoton samun mutum na farko da ya kamu da wannan nau'in na H5N8.

Ba kasafai ake samun mutum ya kamu da cutar murar tsuntsaye ba tun bayan barkewar nau'in H7N9 wanda ya yi ajalin mutum kusan 300 a 2016 da 2017.

Source: BBC