Menu

An yi nasarar tiyatar ƴar shekara 6 da aka yanke wa al'aura a Bauchi

 118016555 53dc6b9c 5644 42b7 Ae62 Edd060465691 Ana rike da matasa biyu da da zargin yanke gaban Hauwa'u Ya'u don yin tsafi.

Tue, 13 Apr 2021 Source: BBC

Gwamnatin jihar Bauchi a Najeriya ta ce an yi nasara wajen tiyatar da aka yi wa yarinyar nan ƴar shekara shida da wasu suka yanke wa al'aura watanni hudu da suka wuce.

Yanzu haka an sallame ta daga asibiti kuma an hada ta da iyayenta kamar yadda hukumomi suka tabbatar wa BBC a ranar Talata.

A cikin watan Janairun wannan shekarar nan ne aka kama wasu matasa biyu masu shekaru 19 da 20 a unguwar Gandu ta karamar hukumar Jama'are, da zargin yanke gaban Hauwa'u Ya'u don yin tsafi.

Duka shekarun Hauwa'u shida, kuma bayanai sun nuna cewa matasan sun ja ta ne cikin wani kango da ke unguwar suka yi mata wannan aika-aika.

To sai dai bayan tsintar ta da wasu mutane suka yi, an garzaya da ita zuwa wani asibiti, inda daga baya Gwamna Bala Muhammad ya sa aka kai ta asibitin koyarwa na Aminu Kano AKTH, don yi mata aiki.

Watanni hudu kenan, sai a ranar Talata wasu hotuna suka fara yawo a shafukan intanet, da suka nuna gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad rungume da ita tana murmushi, bayan ta warke daga wannan jinya.

Dr Aliyu Muhammad Maigoro shi ne kwamishinan lafiya na jihar Bauchi, ya kuma bayyana wa BBC irin fadi tashin da suka yi wurin ceto rayuwar wannan yarinya.

"Da farko an kai ta asibitin da ke kusa da su aka tattare mata jini da farfaɗo da ita saboda ta zub da jini sosai. Daga nan da suka ga aikin ya fi ƙarfinsu sai suka kai ta asibitin koyarwa na Malam Aminu da ke Kano AKTH.

"Bayan an ƙara mata jini sai aka wanke ciwon aka fitar da datti, sai aka kai ta ɗakin tiyata aka yi mata tiyatar sake gyaran gabanta ta hanyar ɓaɓɓago da shi," a cewarsa.

Shi ma Murtala Chanji, wanda ke matsayin mahaifi ga Hauwa'u ya ce: "Gaskiya na yi murna sosai, don ba kowa ne ya yi tsammanin za ta dawo yadda take ba. Amma sai ga shi abubuwa sun gyaru."

Ya yi kira ga iyaye su dinga saka ido kan yara ganin yadda duniya ta zama abar da ta zama.

Cin zarafin kananan yara ta irin wadannan hanyoyi na nema ya zama ruwan dare a Najeriya.

Kamar yadda kididigar hukumar da ke kula da kananan yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna ana cin zarafin yaro daya a cikin kowane uku a Najeriya, ya Allah ta hanyar fyade ko wani nau'in cin zarafin na daban.

Kuma abu ne mai wahala rayuwa ta dawo musu sabuwa kamar yadda Hauwa'u ta yi fitar kutsu a yanzu.

Source: BBC