Menu

Ana iya gano mai ɗauke da COVID-19 ta jin sautin tarin da yayi - Masana

 117674207 Indexpix Nc.png Cutar korona na addaban duniya baki daya

Fri, 28 May 2021 Source: BBC

Masu binciken kimiyyar lafiya a Birtaniya na iya gano wanda ya k dauke da cutar korona ta hanyar jin sautin tarin da ke yi - kuma sakamakon na ƙarfafa gwuiwa.

Masu bincike a Jami'ar Essex sun yi amfani da na'ura mai kwakwalwa tare da ilimin Artificial Intelligence kan mutum fiye da dubu takwas, inda su ka gano cewa manhajar na iya ware masu ɗauke da kwayar cutar kuma ta yi nasara cikin kashi 98 cikin 100 na gwaje-gwajen da su ka yi.

A kan haka, masanan na kokarin samar da wata manhajar da za ta ba duka mai bukatar sanin halin da yake ciki gano ko yana dauke da kwayar cutar ta hanyar yin tari a gaban wayarsa kawai.

Daga nan wadanda manhajar ta bayyana mu su cewa su na dauke da kwayar cutar na iya zuwa dakin bincike domin a tabbatar mu su da sakamakon.

Source: BBC