Menu

Atletico Madrid ta dage sai ta lashe La Liga na bana

 118537546 Atleticosuarez Atletico ta yi nasarar doke Osasuna da ci 2-1 a wasan mako na 37 a La Liga

Mon, 17 May 2021 Source: BBC

Atletico Madrid na daf da lashe kofin La Liga na bana kuma a karon farko a shekara bakwai.

Atletico ta yi nasarar doke Osasuna da ci 2-1 a wasan mako na 37 a gasar ta Spaniya da suka fafata ranar Lahadi.

Sai dai wasan ya kusan zuwa da tangarda, inda Osasuna ta fara zura kwallo ta hannun Ante Budimir, a lokacin Real Madrid na cin Athletic Bilbao 1-0.

Daga baya ne Atletico ta farke ta hannun Renan Lodi, sannan Luis Suarez ya ci na biyu daf da za a tashi daga karawar.

Ta kuma ci kwallayen biyu ne a cikin minti 10 na karshen fafatawar, bayan da aka fara hangen kila ta barar da damar lashe kofin Spaniya na bana.

Tun cikin watan Nuwamba Atletico ta fara dakon teburin La Liga har ta kai ta bayar da tazarar maki 10 tsakani daga baya ta ci karo da cikas.

Atletico ta yi fama da 'yan wasanta musamman masu ci mata kwallaye da suka je jinya, sannan cutar korona ta ci gaba da kama wasu 'yan wasa da dole suka killace kansu.

Barcelona wadda aka yi tunanin tana cikin 'yan takarar La Liga na bana kuma na biyar a kaka bakwai ta yi rashin nasara a hannun Celta Vigo da ci 2-1 a Camp Nou.

Da wannan sakamakon Atletico ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da maki 83, Real ta biyu mai 81, yayin da Barcelona keda 76 da kuma Sevilla ta hudu mai 74.

Sakamakon karawar mako na 37 a gasar La Liga ranar Lahadi:

  • Deportivo Alaves 4-2 Granada


  • Athletic Bilbao 0-1 Real Madrid


  • Atletico Madrid 2-1 Osasuna


  • Barcelona 1-2 Celta Vigo


  • Real Betis 1-0 Huesca


  • Real Sociedad 4-1 Real Valladolid


  • Valencia 4-1 Eibar


  • Villarreal 4-0 Sevilla


  • Getafe 2-1 Levante
  • Cadiz 1-3 Elche


  • Wasannin mako na 38 da za a buga a gasar La Liga ranar 23 ga watan Mayu:

  • Celta Vigo da Real Betis


  • Osasuna da Real Sociedad


  • Real Madrid da Villarreal


  • Sevilla da Deportivo Alaves


  • Real Valladolid da Atletico Madrid


  • Eibar da Barcelona


  • Elche da Athletic Bilbao
  • Levante da Cadiz


  • Granada da Getafe


  • Huesca da Valencia


  • Wadan da ke kan gaba a cin kwallaye a La Liga ta bana:

    1. Lionel Messi Barcelona 30


    2. Gerard Moreno Villarreal 23


    3. Karim Benzema Real Madrid CF 22


    4. Luis Suarez Atletico Madrid 20


    5. Youseff En-Nesyri Sevilla 18
    6. Alexander Isak Real Sociedad 16


    7. Jose Luis Morales Levante 14


    8. Iago Aspas Celta de Vigo 13


    9. Rafa Mir Huesca 13


    10. Kike Garcia Eibar 12


    11. Marcos Llorente Atletico Madrid 12


    12. Antoine Griezmann Barcelona 12


    13. Santi Mina Celta Vigo 12


    Source: BBC