Kungiyar Juventus ta karrama Cristiano Ronaldo da riga mai lamba 770, ta kuma ce shi ne dan wasan da ba a taba yin irinsa ba a tarihi.
Ranar Lahadi, Juventus ta sha kashi a gida da ci 1-0 a wasan mako na 28 a gasar Serie A, kuma a ranar ta karrama kyaftin din tawagar Portugal.
Shugaban Juventus, Andrea Agnelli, shi ne ya bai wa tsohon dan wasan Real Madrid riga mai lamba 770 - wato yawan kwallayen da ya ci a sana'arsa ta tamaula.
Juventus ta kuma yi masa lakabi da "G.O.A.T," greatest of all time da ke nufin dan wasan da ba a taba yin irinsa ba a tarihi.
Ronaldo ya fada cewar ya haura gwarzon Brazil, Pele a yawan cin kwallo 767 ranar 15 ga watan Maris, bayan da ya ci Cagliari kwallo uku rigis.
Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ba ta da sahihin kididdigar kwallon da dan wasa ya ci mafi yawa a tarihin tamaula, amma Ronaldo ya ce shi ne yanzu a kan gaba.
"Ina cike da murna da alfahari da na zama wanda ba a taba yin kamarsa ba a tarihi, kuma ina kan gaba a cin kwallaye a duniya, wanda na haura Pele," kamar yadda ya rubuta bayan wasa da Cagliari.
Sai dai kuma Ronaldo bai ci kwallo ba a karawar da Benevento ta yi nasara a gidan Juventus ranar Lahadi a gasar Serie A.