Menu

'Ba ni da bambanci da matacciya tun da aka cire min ƙwayayen haihuwa'

Premature Births Premature Baby Rahotanni sun nuna ana yawan tilasta kashe kwayoyin haihuwar tsirarun kabilu

Sat, 10 Apr 2021 Source: BBC

Cikin shekaru 20 da suka wuce kasashe 38 sun bada rahoton tilastawa, ko bada kai wajen kashe kwayoyin haihuwa, yawanci kuma an fi tilastawa mata yi ba da son ransu ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran a kawo karshen dabi'ar, wanda abinciken da wani farfesa Sam Rowlands ya gudanar ya gano lamarin ya na shafar al'umma da dama, ana kuma bukatar a hukunta wadanda aka samu da aikata hakan.

Bincike ya gano cewa a fadin duniya, ana tilasta kashe kwayoyin haihuwar tsirarun kabilu, da masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki HIV ko SIDA, da mata maza.

"Akwai dadadden tarihin cin zarafi mai alaka da kashe kwayoyin haihuwa da har yanzu ake ci gaba da yi," inji Dakta Tlaleng Mofokeng, wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan hakkin lafiya.

"Ina ganin wannan shi kadai, mummunan cin zarafi ne."

Tilasta kashe kwayoyin haihuwa wani nau'in azaba ne mai cike da tarihi da sojojin Nazi na Jamsu sukai amfani da shi. Har wa yau, bincike ya gano ba shi da alaka da tarihin da muka karanta kan rahoton abin da ya faru a karni na 21.

Zishilo Dludla ta ce ba ta amince da kashe mata kwayoyin haihuwa ba, lokacin da ta haihu a wani asibiti da ke Afurka ta Kudu a shekarar 2011.

"Kashe min kwayoyin haihuwa babbar mugunta ce a gare ni, saboda ban taba amincewa da hakan ba," inji matar mai shekaru 50 ta na da kuma da 'ya'ya uku. "Ina ma zan manta da abin da ya faru, amma ina hakan bai faru ba. Ba ka da mara ba da mataccen , banbancin kai ka na duniya ne, amma ta wani bngaren an kashe ka.

"Ina kallon kaina matacciya amma a raye, saboda na san ba ni da wata mammora."

Zishilo ta yi amma an yi mata hakan ne saboda ta na dauke da cutar HIV.

"Abin da ke afruwa da yawancin mata shi ne, a asibiti suke kashe musu kwayoyin haihuwa saboda kawai su na dauke da cuta mai karya garkuwar jiki," inji Dakta Mofokeng.

"Dukkansu bakar fata ne, yawanci kuma mazauna karkara. Ana tilasta musu musu rattaba hannu kan yarjejeniyar da amincewarsu za kashe musu kwayoyin haihuwa."

Takardun bayanai na asibitin da aka yi wa Zishilo tiyatar kafin ta fara nakuda, sun nuna ta amince da yi ma ta aikin lokacin da aka cire mata jariri.

Sanarwar ta ce an dauki matakin ne saboda karo biyu ana mata tiyatar cire jariri, kuma nauyin hakan ya rataya a wuyansu na daukar mataki bayan anyi tiyata ta uku, saboda dalilai na lafiyar mahaifiya.

Sun shaidawa BBC: "Ba a tilastawa mata ko yi musu ba da saninsu ba, yawanci na cewa ba sa bukata kuma babu mai tilasta mu su."

Ofishin kula da daidaiton jinsi da aka kafa a shekarar da ta wuce a Afurka ta Kudu na gudanar da bincike kan ikirarin Zishilo da wasu mata masu fama da cutar HIV, na kashe musu kwayoyib haihuwa ba da izininsu ba. Sai dai Dakta Mofokeng ta ce babu wani abu da aka yi tun lokacin.

"Tun daga fannin lafiya da gwamnatin Afurka ta Kudu, sun gaza kare matan ciki har da ofishin da ke ikirarin kawo daidaiton jinsi.

"Sashen kan shi, har yanzu bai amince a bayyane cewa ana aikta wannan mummunar dabi'ar ba ko sanya ido kan hakan."

Ofishin lafiya na Afurka ta Kudu bai maida martani kan bukatar BBC na son jin abin da zai ce kan zargin ba.

Map showing countries where involuntary sterilisations have been reported at childbirth from 2000 to 2018

Haka kuma, a duniya baki daya ba mata masu dauke da cutar HIV kadai ake yi wa ba.

Misali wani rahoton kiwon lafiya na duniya da aka yada, ya nuna mata hudu 'yan asalin kasar Canada sun ce an matsa musu lambar yin tiyata mai alaka da kashe kwayoyin haihuwa tsakanin shekarun

2005 zuwa 2010.

Rahoton ya yi karin haske kan shaidun wasu mata 'yan jamhuriyar Czech Republic, da Hungary da Slovakia da aka matsa musu amincewa da yin tiyatar mintina kadan da haihuwarsu da lokacin da suke shan magani.

A Japan kuma,dole ne ayi wa mata-maza aikin kashe kwayoyin haihuwa, domin a basu damar zabar jinsin da suke son zama. Idan ba a yi musu tiyatar ba, wannan zai janyo musu karancin samun damar yin aure ko sauya jinsinsu a hukumance ta hanar fasfo da sauransu.

A Indiya, ta na sanyawa masu koya wani aiki haraji, da bai wa 'ya'yan iyalan da suke tsarin iyali, ilimi kyauta da nufin rage yawan al'umma. Amma kwararru sun yi allawadai da yin tiyatar, saboda za ta karfafawa marasa karfi kwarin gwiwar yi ko da hakan zai cutar da su.

Rahoton da farfesa Sam Rowlands da Dakta Jeffrey Wale na jami'ar Bournemouth da ke Birtaniya, sun yi ikirarin Indiya na sanyawa ma'auratan da suka ki yin tiyatar takunkumi, misali rike musu katin dan kasa.

Rahoton ya ce mutanen da suka gagara ba da shaidar an yi musu tiyatar ba, ana hana 'ya'yansu su magungunan inganta lafiya da kuzari.

Haka kuma rahoton ya ce an samu shaidun da suka nuna ana bai wa iyalan kyautar talabijin, ko tukunyar saukaka girki ko ma kudi domin su amince ayi musu. Kuma yawanci darajar kayan ta kan rubanya albashi mafi kankanta.

Da wannan misalin na kashe kawyoyin haihuwa na sa kai a duniya Dakta Mofokeng ta ce zai yi wuya gwamnatoci su iya kare hakkin dan adam.

"Akwai tausayawa. Amma ba mu da wani zabi, illa mu tallafi juna. Ni macece, kuma bakar fata, daga yankin karkarar Afurka ta Kudu. Ina da cikakkun bayanan yadda aka yi wa makusanta na ko wadanda na sa ni irin a karkararmu, amma babu wani sauyi," inji ta.

"Aikina na wakiliya ta musamman shi ne tunatar gwamnati hakki ko 'yancin lafiyar mutane, sannan alhaki ya rataya a wuyansu na gudanar da binciken irin wadannan bayanai, tare da hukunta wadanda aka samu da laifi.

"Wannan tiyar keta ce da mugunta, da tauye hakkin matan da ake yi wa hakan, bai kuma kamata mu nade hannu mu zuba ido ana ci gaba da wannan mummunar dabi'ar ba."

Source: BBC