Mai bai wa shugaban Najeriya shawawar kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno ya ce har yanzu ba a san yadda aka yi da makudan kudaden da shugaba Buhari ya bayar don sayen makamai da sauran kayan aiki don yaki da matsallolin tsaro da suka addabi kasar ba.
A hirarsa da BBC Monguno ya bayyana cewa gwamnati na bakin kokarinta wajen shawo kan matsalar tsaron da ake ci gaba da fuskanta, da wasu 'yan Najeiya ke ganin gwamnati ba da gaske ta ke yi ba domin tana ta jan kafa game da al'amarin.
Duk da cewa bai fito kai tsaye ya ce manyan hafsoshin sojan da aka sauke sun cinye kudin sayen makaman ba, amma ya yi jirwaye mai kamar wanka.
Ya ce shi ba zai iya cewa ko wadanda suka yi murabus din sun yi sama da fadi da kudin ba, amma dai abinda zai ce shi ne babu wanda ya san abinda aka yi da kudin tun da har yanzu ba a ga kaya a kasa ba.
A watan janairu ne Shugaban Najeriya ya sauke hafsoshin tsaron ƙasar kuma ya sanar da sabbi.
Hafsoshin sojin sun ƙunshi babban hafsan tsaron ƙasar Janar Abayomi Olonisakin; da babban hafsan sojin ƙasa Janar Tukur Buratai; da babban hafsan sojin sojan ruwa Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; da babban hafsan sojin sama Air Marshal Sadique Abubakar.
Shugaban ya naɗa Janar Leo Irabor a matsayin babban hafsan tsaro da Janar Ibrahim Attahiru a matsayin babban hafsan sojan ƙasa da Rear Admiral Gambo - babban hafsan sojan ruwa sai Air-Vice Marshal Amao a matsayin babban hafsan sojan sama.