Menu

Ban yarda da yi wa ƴan bindiga afuwa ba - Ministan shari'ar Najeriya

 118424003 E93b1f77 Adb3 44b0 8069 33bd12dab45b Ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami

Mon, 10 May 2021 Source: BBC

BBC ta gudanar da wani taron tattaunawa na ke-ke da ke-ke da ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami, inda wasu al'ummar kasar suka samu damar yi masa tambayoyi kan abubuwan da suka shafi tafiyar da harkar shari'a, da cin hanci da rashawa, da harkar tsaro da dai sauran batutuwa.

A lokacin da aka fara tattaunawar wadda aka yi wa lakabi da 'A Fada A Cika' a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ministan ya fara bayyana wa zauren tattaunawar irin gudumawar da ya ce ofishin ministan kuma babban lauyan gwamnati ya bayar wajen magance matsaloli da dama da suka shafi tsaro da cin hanci da rashawa da sauran abubuwa da suka danganci tafiyar da shari'a a kasar.

Cin hanci da rashawa

Ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnati Abubakar Malami ya bayyana wa zauren 'A Fada a Cika ' cewa ofishin na sa ya bayar da gagarumar gudumawa ta fuskar yin fito na fito da cin hanci da rashawa, ta wajen ganin cewa an samu bakin dokoki a mataki na tarayya a kasar.

''An samu bakin tsare-tsare da dokoki ta fsukar cin hanci da rashawa, idan ana maganar wadannan dokoki, sune masu nasaba da hana hada-hadar kudi ta hanyar da ba ta Allah da Annabi ba, lallai an samu bakin dokoki da suka inganta wannan mu'amala,'' in ji ministan.

Game da nuna gaskiya ta fuskar aiki kuma minista Malami ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari karkashin ofishinsa, ta sanya hannu a matakin na tarayya wadda kasashe ne dake tunkaho cewa abinda suke yi ta fuskar za su yi su a bude.

''Haka ne ya sa abubuwan da suka shafi kasafin kudi a gan su a zahiri, saboda tana yin shi a bude, ta sa hannu a dokar da tabbatar da ganin ta kasance tana aiki a kan tsari na budaddiyar gwamnati, wato komai za a yi shi a bude,'' ya ce.

Kimiyya da tsaro

Haka kuma, bayyana wa BBC cewa gwamnatin Najeriya ta samu cigaba ta bangaren kimiyyar tsaro da ta taimaka wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma tsaro.

''An zo da tsare-tsare da suka hada da na samar da lambobin tsaro na asususn ajiyar banki wato BVN, aka tabbatar da cewa sun yi aiki, inda a sanadiyyar hakan ya sa gwamnati ta yi nasarar kama mutane kusan dari bakwai wadanda ake zargi da ya bayyana mai karfi cewa sun yi amfani da kafofin na hada-hadar kudi domin barazana ga abinda tya danganci harkokin tsaron kasa.'' ya ce.

Ministan ya kuma ce gwamnatin shugaba Buharin taka rawar ganin cewa n yaki dacin hanci da rashwa irin su ICPC, EFCC da su Code of Conduct su kasance sun yi aiki wajen sauran nasarori a kan abinda suka danganci aiwatar da hukunci a kan manyan mutanen da a baya ba a isa a taba su ba.

'Yan bindiga da masu satar mutane

Wasu na danganta wannan matsala da rashin ingancin tsarin shari'a a Najeriya ta yadda ba ta hukunta waanda aka kama da aikata masu aikata miyagun laifuka yadda ya kamata.

'Yan Najeriyar da dama na cewa ba kasafai suke ganin ana hukunta wadannan 'yan bindiga ko a gurfanar da su a gaban kotu ba, abinda ya sa ake ganin kamar ma'aikatar shari'ar tana da rauni ko kuma ba ta yi abinda ya kamata ba da ya sa har aka kawo ga wannan yanayi.

Sai dai in ji ministan shari'ar wanda yake mayar da martani game da hakan cewa ba za ka iya yanke hukunci a kan abu ba sai ka dubi mene ne ma'aikatar shari'a ta tarayya ta yi domin ganin cewa an yi maganin damuwa mai nasaba da rashin tsaro gaba daya,

''A shekarar 2017 ofishin babban lauyan gwamnatin Najeriya ya bai wa na jihohi dama su wakilce shi wajen daukar matakai na shigowa gadan-gadan domin aiwatar da shari'oi a jihohinsu'' ya ce.

Ya kara da cewa''Kuma an mun zauna da su, domin a yi nazari game da mafita, bisa la'akari da cewa Najeriya na da yawan al'umma miliyan 200, tana kuma da jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja''.

''Daya daga cikin wannan kudiri da taron namu ya cimma shi ne ya kamata jihohi su bayar da gagarumar gudamawa wajen daukar matakai na shigowa gadan-dagan domin aiwatar da shari'oi a jihohinsu''in ji ministan.

Ban yarda da yi wa 'yan ta'adda afuwa ba

Yayin amsa tambayar da BBC ta yi masa game da wasu gwamnatocin jihohin da suke yi wa masu satar mutane domin neman kudin fansa da 'yan fashin daji afuwa har ma da yi musu hasafi, ya bayyana cewa ba shi da wannan ra'ayin.

''Hakan bai dace ba, duk wanda ya yi ganganci to shi ma a yi masa gangancin, a matsayina na babban lauya gwamnatin Najeriya, bani da tunani na yafiya ga wanda ya mayar da kashe mutum al'ada, ya dauki rayuwar al'umma a bisa gilla,'' in ji ministan.

Ya kuma kara da cewa: "Yan Najeriya miliya dari biyu suna hakkin su zauna lafiya cikin kwanciyar hankali da lumana, don haka idan mutum daya, ko biyu,ko ashirin ko hamsin suka zabi daukar rayukan 'yan najeriya kan tsari na gilla, hakki na ne na ministan shari'a na kasa in mayar musu martani a kan tsari na daukar rayukansu''.

Game da batun da ake yi cewa kamar laifukan da wadannan mutane ke aikatawa gwamnatin tarayya ita ke da hurumi a kai, sannan kuma kamar ba ta dauki wani mataki ba na shari'a, sannna su jihohin suke yafe musu kamar ita gwamnatin Najeriya ta zuba musu ido ba su dauki wasu matakai a kan masu yafewa 'yan bindigar ba.

Amma kuma minsitan ya sake bayyana cewa "Shi yasa na ce a ko wace jiha akwai manyan lauyoyin gwamnati da ya kamata su shigo ciki tare da hukmomin 'yansanda na ko wace jiha, tun da ai bai wa kowanne dama.''

Tambayoyi

BBC ta bai wa wasu daga cikin al'ummar Najeriya da suka halarci zauren taron da kuma wasu da suka rika mika na su tambayoyin ga minsitan ta manahajar Skype damar mika tambayoyin su ga minisan shari'ar.

Tambayoyin dai sun hada da na yanayin yadda gwamnati ke tafiyar da yi wa wadanda aka kama ta aikata laifuka shari'a, da batun dokar 'yancin fadin albarkacin baki, da batun tsaro, da kuma na hanci da rashawa.

Katsalandan a harkar sharia

Malam Kabiru Sa'idu Dakata na cibiyar wayar da kan jama'a kan shugabanci na gari a Najeriya ya tambayi ministan shari'ar game da batun da ya ce zargin da shugaba Muhammadu Buhari ya rika yi wa gwamnatin baya na yin katsalandan a cikin harkokin shari'un da suka shafi zabe, amma kuma bata sauya zane ba bayan da ya zama shugaban kasa'

''Mutane sun yi tsammanin za ta sauya zane bayan da ya zama shugaban kasa, amma kuma yanzu abinda ake gani a Najeriyar irin abubuwab da suka faru a baya ne,'' in ji shi.

Malam Dakata din ya kara kalubalantar ministan game da gudumawar da ya ce ofishinsa ya bayar waje yaki da cin hanci da rashawa, da ya ce amma kuma ya sa aka janye shari'ar da ake yiwa tshon gwamnan jihar Gombe Danjuma Goje kan zargin cin hanci da rashawa da suka shafi biliyoyi naira.

Sannna kuma da batun bayar da umarnin dawo da tsohon shugaban hukumar lura da kudaden fansho ta kasar Abdulrasheed Maina kan mukaminsa duk kuwa da zargin da ake yi masa na badakalar kudade masu yawa a kasar.

''Har yanzu 'yan Najeriya ba su gama gamsuwa da dalilan da suka sa aka janye wannan tuhuma ta tsohon gwamna ba, da kuma maganar dawo da Abdulrasheed Maina kan mukaminsa da aka bayyana ofishinka ya bayar da umarni,'' ya ce.

A daya bangaren kuma minista Malami ya yi misali cewa idan ana magana kan zargen zargen da suka shafi katsalandan ta fuskar mua'malar shari'ar da ta shafi zabe daga bangaren gwamnati amsa mai kyautatuwa ita ce abubuwan da suka faru ta fuskar abinda ya shafi zabe a jihar Zamfara ne.

''Kowa ya sani ta fuskar alkaluman zabe a jihar Zamfara, jamn'iyar APC ita ce kan gaba a kan ko wane kuri'u da suka danganci ko wane zabe da aka gudanar, amma sai aka wayi gari

Malama Habiba Abdulkadir ta gidan rediyon Freedom Kaduna ta tambayi ministan ko ina gaskiyar zargin da aka ce ya yiwa babban Bankin Najeriya a kan wasu kudade saboda yana da muradin wasu kaso daga cikin kudaden.

Amma kuma ministan ya bayyana cewa wannan maganar da ake yi, mu'amala ce da ke da nasaba da hukuncin da aka yanke tun a shekarar 2013 , shekara biyu tun kafin zuwan mulkin shugaba Muhammadu Buhari, a kan cewa a biya wasu kamfanoni kudade.

''Lokacin da gwamnatin shugaba Buhari ta zo a bisa la'akari da yake kudin sun kai biliyan dari biyar da wani abu, ganin cewa suna iya kawo damuwa ga tattali arzikin Najeriyar, shi yasa gwamnai ta yi tunanin cewa an aikata ba daidai ba a kan wannan''.

''Saboda haka ofishin babban lauyan gwamnati ya bayar da umarni zuwa ga ofishin hukumar tsaro ta farin kaya, da hukumar EFCC cewamuna ganin wannan kudin ba halattatu bane, kana hukuncin ba ingantacce bane a bincika,'' in ji Malami.

Ya kuma kara da cewa: ''Wadannan hukumomi sun yi bincike inda suka bayar da rahoton ingancin wadannan kudade, amma a cikin wannan yanayi ofishins ya mstsa a kan cewa a zauna a yi sulhu amma maganar biyan naira biliyan dari biyar da wani abu bata taso ba.''

Ta manahajar Skype kuma, wani lauya mai zaman kan sa dake zama a Birtaniya Bulama Bukarti ya mika tambayrsa a kan abinda ya shafi adalci da daidaito cikin tsarin tafiyar da shari'a ne a Najeriyar.

Kuma ya bayar da misalai kan lokacin da kotu ta bayar da belin tsohon shugaban hukumar fansho ta kasar Abdulrasheen Maina, wanda ya karya dokar belin sa ya gudu.

''Mun ga yadda kuka nemi kotu ta sa aka kamo sanata Ali Ndume wanda ya dauki nauyin belin shi, aka rike shi a kurkuku har sai da Abdulrasheed Maina ya dawo aka sake shi, amma mun ga an kwata irin wannan a shari'ar Nnamdi Kanu da sanata beli Abaribe ya yi belin shi amma ya gudu ya bar kasar, kuma ba mu ji kun sa an kama Abaribe an kulle shi kamar yadda aka kulle Ndume ba,'' in ji Bukarti.

Ya kara da cewa: ''Hakan ne ya sa har yanzu Nnamdi Kanu ya ki dawowa kasar, shin me yasa haka? Ko akwai 'yan bora da 'yan mowa ne a shari'ar da kuke yi? Sannna wai ina labarin Nnamdi Kanu tun da an ayyana kungiyarsa a matsayin ta 'yan ta'adda, an kuma tuhume shi da laifukan cin amanar kasa?''.

Game da wannan tambaya ta Bukarti, ministan ya bayyana cewa matsayin yadda al'amuran shari'a ke tafiya a Najeriya babu dan bora ko dan mowa.

'' Dokar Najeriya tana hawa kan wanda yake cikin Najeriya, idan ya riga tsallake, a dokar kasa ba a daukar mataki ba tare da wasu tsare-tsare na kasa da kasa ba,'' in ji shi. ''Saboda haka idan mutum yana fuskantar Shari'a a Najeriya ya fice ya tafi misali Ingila, doka uku ce za ta yi aiki ta wannan fuskar - dokar Najeriya, ta Ingila, da kuma ta kasa da kasa,'' ya bayyana.

Ƙarin labaran da za ku so ku karanta:

Source: BBC