Joan Laporta ya sake nasara a zaben shugaban kungiyar Barcelona ta Spaniya a karo na biyu.
Laporta, a lokacin yakin neman zabe ya sha alwashin ci gaba da rike Lionel Messi a kungiyar.
Ya samu nasara da kashi 54 cikin 100 a yayin da Victor Font ya zama na biyu sai kuma Toni Freixa na uku.
Dan shekaru 58, shi ne ya nada Pep Guardiola a matsayin kocin kungiyar a lokacin yana shugaba a shekarar 2003 zuwa 2010.
Laporta zai maye gurbin Josep Maria Bartomeu wanda ya yi murabus a watan Oktoban bara.
Shi ne mutumin da ya dauko manyan 'yan wasa kamar su Ronaldinho na Brazil da kuma dan kwallon Kamaru Samuel Eto'o.
A wa'adin mulkinsa na farko, Barcelona ta lashe gasar zakarun Turai sau biyu, da na La Liga sau hudu da kuma na Copa del Rey.