Menu

Barcelona na sa ran cin kofin La Liga na bana

 117588015 Gettyimages 1137660928 Kyaftin din Barcelona Lionel Messi

Tue, 16 Mar 2021 Source: BBC

Barcelona ta yi nasarar doke Huesca da ci 4-1 a wasan mako na 27 a gasar La Liga da suka fafata ranar Litinin a Nou Camp.

Barcelona ta ci kwallayenta ta hannun Lionel Messi da ya ci na farko, sai Antoine Griezmann da ya zura na biyu a raga.

A zagaye na biyu ne Barcelona ta kara na uku ta hannun Oscar Mingueza, sannan kyaftin, Messi ya kara na hudu kuma na biyu da ya ci a karawar.

Ita kuwa Huesca ta zare kwallo daya ta hannun Rafa Mir a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Kawo yanzu Messi ya ci kwallo 21 a gasar La Liga ta bana, kuma shi ne kan gaba a takarar takalmin zinare da ake kiran kyautar Picici a gasar ta Spaniya.

Haka kuma Messi ya yi kan-kan-kan da Xavi a tarihin yawan buga wa Barcelona wasanni, wanda ya yi karawa ta 767 a kungiyar.

Shi kuwa Griezmann ya kawo kanfar cin kwallaye a karon farko a gasar, wanda rabon da ya zura kwallo tun bajintar da ya yi a wasa da Athletic Bilbao a karshen watan Janairu da Barca ta ci 2-1.

Kuma kwallon farko da ya ci wa Barcelona tun biyun da ya zura a ragar Granada ranar 3 ga watan Fabrairu a Copa del Rey da Barcelona ta yi nasara da ci 5-3.

Da wannan sakamakon Barcelona ta koma ta biyu da tazarar maki hudu tsakaninta da Atletico Madrid ta daya da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid ta uku a teburi, bayan wasa 27 a gasar bana.

Tuni dai Paris St Germain ta fitar da Barcelona daga Champions League na bana, yayin da kungiyar Nou Camp wadda ta kasa cin kofi a bara ke fatan lashe La Liga da Copa del Rey da ta kai wasan karshe.

Source: BBC