Barcelona ta yi nasarar doke Getafe da ci 5-2 a wasan mako na 31 a gasar La Liga da suka kara ranar Alhamis a Camp Nou.
Minti takwas da fara wasa kyaftin Lionel Messi ya ci kwallo, sai dai minti hudu tsakani Getafe ta farke, bayan da Clement Lenglet ya ci gida.
Kungiyar ta Camp Nou ta kara na biyu a raga, bayan da Soufiane Chakla ya ci gida a minti na 28 da take leda.
Saura minti 12 su je hutu ne, Barcelona ta kara kwallo na uku ta hannun Messi, kuma na biyu da ya ci a wasan.
Sai dai kuma Getafe ta zare kwallo ta hannun Enes Unal a bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti na 69.
Saura minti uku a tashi daga fafatawar Barcelona ta ci kwallo na hudu ta hannun Ronald Araujo.
Daga karshe Barcelona ta ci na biyar a bugun fenariti ta hannun Antoine Griezmann.
Rabon da dan kwallon Faransa ya ci wa Barcelona kwallo a gasar La Liga tun 21 ga watan Maris a wasan da Barca ta doke Sociedad 6-1.
Sai dai ya zura kwallo a ragar Bilbao da Barcelona ta lashe Copa del Rey ranar 17 ga watan Afirilu.
Da wannan sakamakon Barcelona wadda ta yi wasa 31 ta koma ta uku a kan teburi da maki 68.
Atletico Madrid mai maki 73 ta ci gaba da jan ragamar teburin, bayan da ta doke Huesca 2-0 a wasan mako na 32 ranar Alhamis.
Real Madrid wadda ta buga wasa 32 tana ta biyu da maki 70, bayan da ta ci Cadiz a ranar Laraba.