Menu

Barcelona ta rage albashin Messi, Man City za ta sayar da Sterling

 118287318 0f363df8 7c8a 4189 A45c C2b833bc99b1 Lionel Messi, kyaftin Barcelona

Sun, 2 May 2021 Source: BBC

Dan wasan Argentina na gaba Lionel Messi, mai shekara 33, ya amince Barcelona ta rage masa albashi domin ta samu damar sayen sabbin 'yan wasa kamar, Erling Braut Haaland na Borussia Dortmund. Messin zai fara tattaunawa da Barca a kan sabuwar yarjejeniyar da za su kulla. Kuma kungiyar ta gaya masa za ta fara cinikin Haaland dan Norway mai shekara 20. (Jaridar Eurosport)

Ita ma kungiyar Manchester City ta ce a shirye take ta siyar da dan wasanta na gaba, dan Ingila Raheem Sterling, mai shekara 26, a bazaran nan, domin ta samu kudin sayen sabbin 'yan wasa irin su Haaland na Borussia Dortmund da kuma dan wasan tsakiya na Aston Villa, dan Ingila Jack Grealish, mai shekara 25 a bazaran nan. (Jaridar Football Insider).

Chelsea za ta yi gogayya da Barcelona wajen neman sayen Adrien Rabiot daga Juventus a bazaran nan, inda kungiyar ta Italiya ta yi wad an wasan na tsakiya na Faransa mai shekara 26 farashin fam miliyan 17. (Jaridar Calciomercato)

Leicester ta bi sahun Aston Villa da Wolves a zawarcin dan wasan gaba na Ingila Tammy Abraham, mai shekara 23, daga Chelsea a bazaran nan. (Jaridar Football Insider)

Haka su ma kungiyoyin West Ham da Newcastle na daga cikin kungiyoyin da ke sha'awar Abraham, inda Chelsea ta ce za ta iya karbar fam miliyan 40 a kan dan wasan. (Jaridar ESPN)

Dan wasan tsakiya na Arsenal, dan Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 25, ba zai ci gaba da zaman aro ba a Atletico Madrid a shekara ta biyu, domin zai tafi Boca Juniors. (Jaridar Mundo Deportivo)

Leicester da AC Milan da kuma Wolfsburg na sa ido a kan dan wasan gaba na Le Havre Josue Casimir, mai shekara 19. (Jaridar Foot Mercato)

Juventus za ta bukaci Massimiliano Allegri, mai shekara 53, ya koma ya maye gurbin dan uwansa dan Italiya Andrea Pirlo, mai shekara 41 a matsayin mai horad da kungiyar a bazaran nan (Jaridar Gazzetta dello Sport)

Batun yawan albashin da Arturo Vidal ya bukata ya dakatar da tattaunawar cinikin dan wasan na Chile mai sheaka 33 daga Inter Milan zuwa Marseille. (Jaridar Calciomercato)

Dan gaban Sifaniya Lucas Vazquez na dab da kulla sabuwar yarjejeniya da Real Madrid, duk da bukatar da Bayern Munich da Paris St-Germain ke yi a kan wasan mai shekara 29 wanda zai kasance ba shi da kungiya a bazaran nan. (Jaridar AS)

Watakila Newcastle ta nemi sayen dan wasan tsakiya na Huddersfield Lewis O'Brien, mai shekara 22, a matsayin zabi mai sauki maimakon Joe Willock na Arsenal mai shekara 21 da ke zaman aro. (Jaridar Sun)

Aston Villa za ta sayi sabon dan baya a bazaran nan domin kintsa bayanta, yayin da take shirin sayar da dan bayan kasar Belgium Bjorn Engels, mai shekara 26. (Jaridar Football Insider)

Source: BBC