Ana ci gaba da zaman fargaba a yankin kudu maso gabashin Najeriya, inda ake samun ƙaruwar hare-haren da wasu da ake zargin masu fafutukar kafa kasar Biafra na IPOB ne ke kai wa jami'an tsaro a ofisoshinsu.
Batu na baya bayan nan shi ne wanda wasu da ake zargin mayaƙan na IPOB ne suka ƙona wani ofishin 'yan sanda a ƙaramar hukumar Onicha da ke jihar Ebonyi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani jami'in tsaro ɗaya.
Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC Hausa cewa ko da yake jami'i daya ne za a iya cewa ya mutu, amma babu tabbacin ko shi kadai ne ko akwai wasu.
''Ƴan bindigar kan kwashe makaman jami'an tsaro idan suka kai hari suka kashe su, don haka a halin da ake ciki mutane na cikin zullumi da fargaba saboda rashin abin da zai iya faruwa a kowanne lokaci.
A jihar Imo, wato inda lamarin ya faro nan ma haka abun yake, wani mazaunin birnin Owerri ya shaida mana cewa har yanzu mutane sun kasa sakewa tun bayan harin da 'yan bindigar suka kai gidan yari tare da sakin ɗaurarru a kwanakin baya.
Ya ce akwai motocin sintiri na jami'an tsaro da tankokin yaƙi suna yawo a gari domin tabbatar da tsaro a fadin jihar baki daya.
A cewarsa ''su kansu sojan a tsorace suke ballantana mu jama'ar gari, da ka ƙirga shago ɗaya ko biyu za ka ga na uku a rufe, komai ya tsaya cik saboda fargabar da ake ciki a wannan lokaci.
Can ma jihar Abia wadda ke wannan yanki na kudu maso gabashin Najeriya ma bata sauya zani ba, domin harkokin kasuwanci sun tsaya ba zirga zirga kamar yadda aka saba, kamar yadda BBC Hausa ta samu bayanai.
Wani mazaunin birnin Aba ya ce bai wuce kashi 40 cikin 100 na harkokin kasuwanci ake yi ba, sakamakon dokar da mahukunta suka kafa ta talkaita zirga-zirga.
''Sojoji ne suka fi zagawa sosai, su 'yan sanda sun kasa sun tsare ne a ofisoshinsu, domin kare hare haren da ake yawan kai musu''
Ya ƙara da cewa ''Daga ƙrfe 8 zuwa 9 na dare za ka ga kowa ya shige gida babu kowa a tituna.
Wani batu da ke kara tayar da hankali shi ne ganin yadda ba wai ofisoshin 'yan sanda kawai ake kaiwa harin ba, har ma da sauran gine-ginen gwamnati.
Wasu bayanai na cewa ko da a ranar Asabar, sai da maharan suka cinna wa ofishin hukumar zaɓen Najeriya wato INEC wuta a jihar Akwa Ibom.