Manufofin kasar China na mayar da dubban 'yan kabilar Uighur da sauran kananan kabilu a birnin Xinjiang zuwa sabbin wuraren ayyuka nesa da gida yana haifar da raguwar yawansu, kamar yadda wani cikakken bincike na kasar China da BBC ta gano ya nuna.
Gwamnati ta musanta cewa tana yunkurin sauya alkaluman yawan al'ummar yankinta na yammaci mai nisa, sannan ta ce sauye-sauyen wuraren aikin an tsara ne saboda samar da kudaden shiga da kuma shawo kan matsalolin rashin aikin yi da talauci.
Amma bincikenmu ya nuna cewa - hade da sansanonin sake ilimantarwa da aka kafa a fadin birnin Xinjiang a shekarun baya - manufofin sun kunshi babbar barazanar tursasawa kana an kuma tsara ne don a sauya wa kananan kabilu tunani da kuma tsarin tafiyar da rayuwarsu.
Binciken, wanda aka yi domin manyan jami'an gwamnati kadai su gani amma aka yi kuskuren yada wa a shafin intanet, ya zama wani bangaren binciken BBC kan farfagandar rahotanni da hirarraki, da ziyarce-ziyarcen masana'antu a fadin kasar China.
Mun kuma yi tambaya game da yiwuwar akwai alaka tsakanin sauya wa 'yan kabilar Uighur ayyukan yi da kuma manyan kayyaki biyu da aka sarrafa a yammacin kasar.
A wani kauye a kudancin a Xinjiang, ana tattaro ciyayi a gonaki kana iyalai kan rika dora kayan marmari da gurasa a kan daben da galibi al'adu da rayuwar iyalai 'yan kabilar ke ta'allaka a kai.
Amma kuma iskar da ta ke kadawa a fadi hamadar Taklamakan na haifar da babbar damuwa da kuma sauyi.
Rahoton faifen bidiyo da tashar talabijin da jam'iyar kwaminist ta kasar China ke tafiyarwa, ya nuna wasu jami'an gwamnati a tsakiyar kauyen, zaune a karkashin wata jar tuta suna tallata samar da ayyukan yi a lardin Anhui, mai nisan kilomita 4,000 daga birnin.
Bayan kwanaki biyu cif, rahotanni sun ce babu koo da mutum daya daga kauyen da ya fito don rattaba hannu, don haka jami'an sai suka fara bi gida-gida.
Abin da ya biyo baya shi ne wani faifen bidiyo mai daukar hankali na gagarumin gangamin kasar China na mayar da 'yan kabilar Uighur da Kazakh da sauran kananan kabilu a Xinjiang zuwa yin ayyuka masana'anta da kuma aikin hannu, a wuraren da ke da tsananin nisa da gidajensu.
Duk da cewa an yada ne a shekarar 2017, lokacin da aka fara tsaurara manufofin, har yanzu ba a yada faifen bidiyon a labaran kafafan yada labaran kasashen waje ba.
Jami'an sun yi magana da wani uba wanda a bayyane ta ke yana dari-dari da barin 'yarsa Buzaynap ta tafi wani wuri mai nisa.
"Akwai wani na daban da yake son zuwa can, ya yi kokarin rokon su,' Za mu iya tafiyar da rayuwarmu a nan, ku kyale mu mu zauna a nan.''
Sun yi magana kai tsaye da Buzaynap mai shekaru 19, suna mai fada mata cewa muddin ta tsaya za a yi mata aure ba da dadewa ba kuma ba za ta iya barin wurin ba.
"Yi tunani dai, za ki iya tafiya can?" suka tambaya.
A karkashin sa idon jami'an gwamnatin da ma'aikatan gidan talabijin ta girgiza kai ta amsa cewa, "Ba zan je ba."
Matsin lambar ta cigaba har sai daga karshe cikin kuka ta amince.
"Zan tafi idan sauran ma suka tafi,'' ta ce.
Fim din ya kawo karshe da bankwana cike da kwalla tsakanin iyaye mata da 'yaya mata yayin da Buzaynap da sauran irinta ma'aikatan da aka ''tattara'' suke barin danginsu da al'adunsu a baya.
Farfesa Laura Murphy wata kwararriya ce a fannin harkokin kare hakkin ɗan adama da kuma aikin bauta na zamani da ke Jami'ar Sheffield Hallam a Birtaniya, wacce ta zauna a Xinjiang tsakanin shekarar 2004 da 2005 kuma tun lokacin ta kan zaiyarci yankn.
"Wannan faifen bidiyo abu ne mai kyau," kamar yadda ta shaida wa BBC.
"Gwamnatin kasar China ta ci gaba da ikirarin cewa mutane a bisa radin kansu ne suka shiga cikin wadannan shirye-shirye, amma wannan tabbas ya bankado cewa an tursasa wa mutane ne ta yadda ba za su iya kin amincewa ba."
"Daya bangaren da ya nuna kuma shi ne wata boyayiyar manufa,'' in ji ta.
Duk da cewa labaran duk a kan fitar da mutane daga kangin talauci ne, akwai yunkurin sauya rayuwar mutane, don raba su da danginsu da rage yawan al'umma da sauya harsunansu da al'adunsu da tsarin tubalin ginin iyalinsu, wanda akwai yiwuwar kara haifar da talauci a maimakon rage shi."
Za a iya bayyana salsalar yadda kasar China ta tunkari salon mulkinta da mataki kan yankin na Xinjiang tun lokacin da aka kai wasu munanan hare-hare kan masu tafiya a bakin hanya da kuma masu tuka ababan hawa.
A birnin Beijing cikin shekarar 2013 da kuma birnin Kunming cikin shekarar 2014 - da aka dora alhakin faruwar hakan a kan 'yan kabilar Uighur masu tsattsuran ra'ayin addinin Isalama kuma 'yan aware..
Wannan daukacin manufa ta mayar da 'yan kabilar Uighur cikin al'adun Han mafiya rinjaye a kasar China ya fito fili daga rahoton cikakken binciken kasar China kan tsarin sauya wuraren ayyukan Xinjiang da aka rarraba wa manyan jami'an gwamnatin kasar wanda kuma BBC ta samu.
An kuma yi kuskuren yada rahoton a bainar jama'a a shekarar 2019 zuwa watanni kadan bayan nan.
Rahoton binciken wanda wasu 'yan Boko suka rubuta daga Jami'ar Nankai da ke birnin Tianjin na kasar China, ya karkare da cewa sauya wa ma'aikata wuraren aikin na da ''tsari ne mai matukar muhimmanci wajen hade 'yan kabilar Uighur marasa rinjaye'' tare da gyara tunaninsu."
Tsame su da kuma sauya musu wurin zaman zuwa wani yanki ko kuma wasu larduna na kasar China, ya ce ''zai rage yawan al'ummar kabilar ta Uighur.''
Wani mai bincike dan kabilar Uighur da ke zaune a kasashen waje ne ya gano rahoton a shafin intanet.
Dr Adrian Zenz, na cibiyar kula da kuma tallafa wa wadanda mulkin kwaminisanci ya shafa a Washington, ya rubuta na shi fashin bakin game da rahoton ta ya hada da fassararsa cikin harshen Turanci.
"Wannan cikakku kuma sahihan bayanai ne da manyan 'yan Boko kuma tsofaffin jami'an gwamnati suka rubuta, kuma masu cikakkiyar masaniya game da ita shi kansa yankin nan Xinjiang," Dr Zenz ya bayyana wa BBC.
Fashin bakinsa sun hada da ra'ayi game da doka da shari'a daga Erin Farrell Rosenberg, tsohon babban mai bayar da shawara ga cibiyar ajiyar kayan tarihi Holocaust Memorial Museum ta Amurka.
cewa rahoton na Nankai ya samar da sahihan shaidu" kan laifukan da aka aikata kan bil adama na gallazawa da tilsata musu barin wurarensu na asali ya zuwa wasu yankuna masu nisa.
A wata sanarwa a rubuce, ma'aikatar harkokin wajen China ta ce, "Rahoton na dauke da ra'ayin marubutan ne kawai, da kuma cewa akasarin abubuwan da ya kunsa ba su bi hanyar gaskiya ba.''
"Muna fata manema labarai za su yi amfani da sahihan bayanan da gwamnatin China ta fitar a matsayin hanyar bayar da rahotanni kan Xinjiang."
Marubuta rahoton na Nankai sun rubuta a kan yunkurin shawo kan matsalar talauci ta hanyar sauya wuraren aikin, kuma ya zuwa masana'antu da ka amince wa ma'aikatan ''yancin ficewa da kuma dawowa.''
Akwai matsin lamba wajen kokarin cimma burin da ake da shi, bayan kafa cibiyoyin daukar ma'aikata a ko wane kauye, da kuma jami'an gwamnatin da aka dora wa alhakin hada kawuna da jan hankulan mutane, da kuma bi gida-gida,'' kamar yadda aka yi wa Buzaynap mai shekara 19.
Akwai alamun tursasawa ga wadanda aka dauka aikin da aka kwashe su da yawa aka tafi da su zuwa masana'antu - a wasu lokuta har mutum dari a lokaci guda."
Manoma da ba za su iya barin gonakinsu ko dabbobinsu ba, ana karfafa musu gwuiwa su mayar da su zuwa tsarin gwamnati da zaiiya lurar musu da su a lokacin da ba sa nan.
Kuma da zarar sun isa masana'antun don fara sabbin ayyukan na su, ana saka ma'aikatan a karkashin wani tsarin mulki na bai daya da jami'an ''su ci su kuma zauna tare da su.
Amma kuma rahoton ya yi nuni da cewa nuna wariya a bisa tsarin ba haifar da cikas wajen samu cigaban da ake bukata, bayan da ta wani gefen 'yansandan yankin gabashin China suna sa ido kan isowar babbar mota makare da 'yan kabilar Uighurs, da a wasu lokuta a kan mayar da su baya.
Kamfanin sarrafa tufafi na Huafu na gefen yankin rukunin masana'antu a birnin Huaibei, da ke lardin Anhui na gabashin China.
Masana'antar da aka tura Buzaynap wacce aka nuna a gidan talabijin na kasar.
Lokacin da BBC ta kai ziyara, dakin kwana na daban na 'yan kabilar Uighur mai hawa biyar, ya nuna alamu kadan na cewa akwai masu kwana a cikin, baya ga wasu takalma da aka dora a kan wata budaddiyar taga.
A bakin babbar kofar shiga, mai gadin ya ce ma'aikata 'yan Uighur "sun koma gida," ya kara da cewa saboda kokarin rage yaduwar cutar korona a kasar, kana a wata sanarwa Huafu ya shaida mana cewa, "kamfanin yanzu ba ya daukar ma'aikata daga yankin Xinjiang ."
BBC ta iya gano wasu rigunan matashin kai da aka yi daga yadunan kamfanin Huafu a shafin intanet na kamfanin dillancin da kaya ta yanar gizo Amazon na kasar Birtaniya, duk da cewa ba mai yiwuwa bane a tabbatar ko kayan suna da alaka da masana'antar da muka ziyarta, ko kuma daya daga cikin kayaiyakin kamfanin.
Amazon ya shaida wa BBC cewa ba ya amincewa da tlasta yin aiki kwadago kana kuma a duk inda ta gano kayan da ba su dace da tsarin sayar da kaya na kamfanin ba, yana cire su daga shagon.
BBC ta yi aiki tare da wasu 'yan jaridar kasashen waje da ke zaune a kasar China, inda suka ziyarci masana'antu shida a tsakaninmu.
A masana'antar kere takalma ta Dongguan Luzhou da ke lardin Guangzhou, wata ma'aikaciya ta ce ma'aikata 'yan kabilar Uighur na amfani da wuraren kwana da wuraren cin abincinsu daban, kana wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa kamfanin na kera wa kamfainin Sketchers na Amurka takalman.
An dade ana bayyana alakar masana'antar da kuma kamfanin na Amurka, da wasu faya-fayen bidiyo a shafukan sada zumunta da ba a tabbatar da sahihancinsu ba wadanda ke nuna ma'aikata 'yan kabilar Uighur na kera takalma kirar Skechers, kana yana nuna alamar dangantakar a wani shafin harkokin kasuwancin intanet na kasar China.
A wata sanarwa, kamfanin na Skechers ya ce "ba ya goyon bayan tursasa yin aikin kwadago," amma bai amasa tambayoyi kan ko yana amfani da kamfanin na Dongguan Luzhou a matsayin mai kerawa da samar musu da kaya ba.
Kamfanin na Dongguan Luzhou dai bai mayar da martani game da batun ba.
Hirarrakin da aka nada a wurin sun nuna cewa ma'aikata Uighur na da 'yancin fita daga masana'antar lokacin hutawa, amma a wasu masana'antun da muka ziyarta don gudanar da binciken, shaidar ta kasance daban.
A akalla abubuwa kashi biyu, an shaida wa manema labarai wasu ka'idoji, kana a wani kamfanin a birnin Wuhan wan ma'aikaci dan kabilar Han ya shaida wa BBC cewa an haramta wa abokan aikinsa 200 'yan kabilar Uighur fita daga ciki.
Watanni bayan da aka Buzaynap na barin kauyenta don ta fara karatunta na horarwa, ma'aikatan gidan talabijin na kasar China sun sake ganawa da ita, wannan karon a kamfanin sarrafawa da sayar da tufafi na Huafu a birnin Anhui.