Menu

Boko Haram: 'Akwai shakku kan sahihancin bidiyon harbi jirgin sojin Najeriya'

Nigeria Airforce Fighter Jet Boko Haram ta ce ita ta harbi jirgin sojin saman Najeriya

Sat, 3 Apr 2021 Source: BBC

Masana harkar tsaro sun yi tsokaci game da ikirarin Kungiyar Boko Haram cewa ita ce ta harbo jirgin sojin saman Najeriya da a ranar Juma'a hukumomin kasar suka ce ya fadi ne.

Tun farko dai rundunar sojin saman kasar ta fitar da sanarwar cewa jirgin kirar NAF 745 bata ya yi kuma ana ci gaba da binciken lalubo shi da matukan jirgin.

Barista Audu Bulama Bukarti, mai bincike kan harkokin tsaro a Afirka ya shaida wa BBC cewa fitar da bidiyon da Boko Haram ta yi ba shi ne zai tabbatar da sahihancinsa ba saboda "akwai yanke-yanke da hade-hade a cikinsa".

Sai dai masanin ya yi ayar tambaya kan yadda ƴan Boko Haram suka san inda jirgin ya fadi "har suka riga sojojin Najeriya zuwa wajen dai-dai lokacin da sojojin Najeriya suke ta neman jirgin har su suka dau bidiyo suka (yaɗa)".

Ya bayyana cewa matukar jirgin da Boko Haram ɗin ta yi ikirarin harbowa ya kasance jirgin da rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana ya faɗi, hakan yana nuna hadarin da ake ciki a kasar.

Masanin ya ƙara da cewa ba abin mamaki bane cewa Boko Haram ta harbo jirgi saboda "a watan da ya gabata sun harbo makami mai linzami daga wajen Maiduguri ya fada cikin (birnin) har ya kashe mutum 16 ciki har da yara tara suna wasa a filin ƙwallo".

Ana maganin kaba, kai na kara kumbura ...

A cewar Barista Bukarti matsalar yaƙi da Boko Haram a Najeriya ta yi kama da karin maganar da ke cewa ana maganin kaba, kai na kara kumbura ganin yadda matsalar ke ci gaba da ta'azzara.

Ya ce abin takaici a wajensa shi ne yadda gwamnatin Najeriya a kullum take kokarin nuna matsalar bata da girma - "sojoji sun fitar da sanarwa cewa bidiyon da Boko Haram ta fitar karya ne kamar suna nuna jirgin da kansa ne ya fadi".

A ganinsa, ya kamata gwamnati ta amince akwai matsala kuma ta yadda cewa "mutanen nan suna da makamai da kayan aiki na zamani kuma a yi kokarin magance wannan ta hanyar kara amfani da soja da dabarun yaki".

Source: BBC